Yadda za mu tarbi watan Ramadan mai albarka
Imam Murtada Muhammad Gusau, Babban Limamin Masallacin Nagazi-Ubete, Okene, Jihar Kogi Mukaddima: Bayan haka, ya ’yan uwana! Ramadan na daya daga cikin watannin da ake haba-haba da zuwansa a cikin watannin Musulunci. Wata ne da ke cike da alherai da rahamomin da Allah Yake saukarwa a kan Musulmi. Domin Musulmi su kara samun rabo […]
Imam Murtada Muhammad Gusau, Babban Limamin Masallacin Nagazi-Ubete, Okene, Jihar Kogi
Mukaddima:
Bayan haka, ya ’yan uwana! Ramadan na daya daga cikin watannin da ake haba-haba da zuwansa a cikin watannin Musulunci. Wata ne da ke cike da alherai da rahamomin da Allah Yake saukarwa a kan Musulmi. Domin Musulmi su kara samun rabo daga wadannan alherai da rahamomi, akwai bukakar su kintsa kansu domin yin maraba da watan ta yadda za su shiga cikinsa cikin sauki tare da gudanar da ayyukan alheri masu yawa a daukacin watan.
’Yan uwa maza da mata! Yana da kyau Musulmi ya kintsa wa zuwan watan Ramadan tare da shirin aikata dukkan ayyukan kirki da ake so a cikinsa domin samun alherai da rahamomin cikinsa. Hudubarmu ta yau za mu duba muhimmancin watan Ramadan ne da hanyar da Musulmi za su tunkare shi tare da kintsa masa kafin ya iso.
Muhimmancin Ramadan: Ya bayin Allah! Akwai ayoyin Alkur’ani da hadisan Annabi (SAW) da dama da suka yi magana kan muhimmancin Ramadan a Muulunci. Aya mai zuwa ta bayyana muhimmancin Ramadan kamar haka:
“Ya ku wadanda suka yi imani! An wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan wadanda suke daga gabaninku, tsammaninku za ku yi takawa.” (K:2:183).
Daga wannan aya ta Alkur’ani za mu fahimci cewa azumi ba sabon abu ne ko wani abu na musamman da aka kebe Musulmi da shi, maimakon haka al’ummomin annabawan da suka gabata ma sun yi azumi. Kuma a wannan aya Allah Madaukaki Ya bayyana manufar yin azumin watan Ramadan wato mutane su samu takawa. Don haka azumi yana da muhimmanci ga Musulmi domin yana tsarkake ruhinsa tare da kai shi ga wani matsayi na takawa.
Abin lura game da Ramadan: Ya ’yan uwana! Duk lokacin da watan Ramadan ya zo, abu na farko da ake so mutum ya yi shi ne ya yi nazari kan manufar azumin watan Ramadan. Allah Madaukaki ba Ya bukatar azumin kansa, ba Ya bukatar kishin ruwa ko yunwar wani Musulmi, maimakon haka azumin yana amfanar shi Musulmi ne da sauran al’umma.
Kuma duk da cewa a ayar da muka ambata Allah Madaukaki Ya ambaci manufar azumi cewa don Musulmi ya samu takawa. Duk da haka akwai wasu dalilai da za a iya nazari kansu da za su iya kawo wasu manufofi na daban.
Na daya, a cikin watan Ramadan, dukkan Musulmi kan gudanar da ibadoji yadda ya kamata, don haka sananne ne cewa wannan wata yana bayar da damar dada samun lada da samun gafara kan zunubban da aka gudanar.
Na biyu, yunwa da kishin ruwan da ake sha a watan Ramadan suna taimaka wa Musulmi ya tuna da sauran mutanen duniya da ba su iya samun wadataccen abinci ko ruwan sha. Idan Musulmi yana yin azumi zai rika tuna wadancan mutane ya rika jin abin da suke ji da yadda suke samun kansu na karancin kayan masarufi.
Na uku, a duk lokacin da Musulmi ya samu kansa a cikin rashin karfin jiki, duk da cewa yana shafar yanayin jiki, amma hakikanin abin da hakan ke haifarwa shi ne gyara halin mutum ya zamo mai saukin kai da tawali’u da hakuri. Don haka a lokacin azumi, ana sa fata Musulmi ya yi kokarin kyautata halayensa wajen hakuri da tawali’u.
Kuma ina ba ku shawara ku yi kokari ku san umarni da hani kan azumin watan Ramadan yadda ya kamata domin kauce wa aikata munanan abubuwa da kuma aikata kyawawa.
Kintsa wa Ramadan: Musulmi sukan yi haba-haba da isowar Ramadan ta yadda za su rika gudanar da ayyukan ibada tare da samun dimbin albarka da rahama da gafarar Allah Madaukaki. Isowar Ramadan na kawo cikakken sauyi ko manyan sauye-sauye kan yadda mutum ke gudanar da rayuwarsa. Don haka wadanda ba su kintsa wa zuwansa ba, sukan sha wahalar gudanar da ayyukan da Ramadan yake bukata a yau da kullum idan ya zo. Saboda haka manufar kintsawar ita ce mutum ya samu damar canja rayuwarsa zuwa daidai da rayuwar Ramadan domin kada ya yi asarar lokacinsa mai tsada. Bari in kawo manyan misalan abubuwan da za su taimaka wajen kintsa kanka domin samun alheran da suke cikin wannan wata mai girma.
Kyakkyawar niyya: Farkon abin da ake bukatar Musulmi ya yi game da kintsa wa Ramadan shi ne kyakkyawar niyya. Sai ka yi niyyar aikata karin ayyukan alheri a wannan wata, za ka iya jin dadin Ramadan tare da samun alheran da yake kawowa. Amma idan kawai burinka ka shiga wata ka fice ba tare da aikata wani aikin alheri na daban ba, ko ka tsara yadda kawai za ka samu sauki ga kanka, to da wuya ka ci gajiyar Ramadan kuma yana iya zama mai wahala gare ka. Don haka yi kyakkyawar niyya game da kintsa wa watan.
Sabo da yawan tasbihi: Tasbihi shi ne yabon Allah Madaukaki da baki ko harce da Musulmi zai yi ta hanyar wasu jimloli ko kalmomi na ambaton Allah Madaukaki. A cikin watan Ramadan kowane lokaci na da muhimmanci, don haka idan mutum yana son samun lada mai yawa a ranakun Ramadan baya ga salloli, abin da ya fi dacewa Musulmi ya yi shi ne ya yi ta Tasbihi. Idan ka fara Tasbihi wata daya kafin zuwan watan albarka na Ramadan, lokacin da watan zai zo tuni ka saba da yin Tasbihin, kana zaune ne ko kana tafe ko kana yin wani aiki.
Yin salloli a kowane lokaci: Ya ’yan uwa maza da mata! A watan Ramadan, mutanen da suke halartar Sallah a cikin jama’a suna karuwa. Akwai mutanen da a farko sukan sha wahala kafin su samu su je masallaci domin yin Sallah a cikin jama’a a farkon ranakun Ramadan. Domin ka tabbatar ka rika yin Sallah a cikin jama’a a ranakun farko na Ramadan, ka fara zuwa salloli cikin jama’a tun kafin Ramadan ya iso. Ga wadanda ba su san yadda ake yi Sallah yadda ta kamata ba, suna iya tuntubar malamai ko wadansu da suke kusa da su ka yadda ake Sallah mataki-mataki, ko su yi amfani da hanyoyin sadarwa na zamani da ke wayoyinsu wajen dada fahimtar haka.
Kokarin yin azumin nafila: Farkon azumin Ramadan kan zama mai wahala ga wadansu Musulmi, domin sukan hadu da yunwa da kishin ruwa ne kwatsam saboda ba su saba ba, kuma ba su san yadda za su wuni da karancin abinci ba. Ba su san yadda za su sauya rayuwarsu game da cin abinci ko kishin ruwa ba. Yin azumin nafila ga irin wadannan kafin Ramadan zai taimaka musu kan yadda za su san sauye-sauyen da ke zuwa lokacin azumin ta yadda idan Ramadan ya zo sun kintsa masa.
Karatun Alkur’ani: Karanta Alkur’ani na kawo albarka da alheri da lada mai yawa daga Allah Madaukaki; don haka yana da kyau Musulmi ya samu isasshen lokaci na karanta Alkur’ani. Ya tabbatar ya rika karanta Alkur’ani a Ramadan, kuma ya tabbatar ya saba da karatunsa kafin Ramadan ta yadda zai saba da karatunsa ko Ramadan ya zo. Wadanda ba su iya karanta shi cikin Larabci wannan ne lokaci mafi dacewa da za su fara koyonsa, saboda koyon karatun Alkur’ani a Ramadan yana da lada fiye da sau saba’in a kan koyonsa a wani wata na daban. A takaice yana da muhimmanci ga Musulmi ya kara zage dantse wajen sanin manufar azumin Ramadan ta yadda zai dada gogewa da aiwatar da wadancan manufofi a rayuwarsa. Kuma sananne ne cewa kintsa wa wannan wata mai girma yana taimaka wa mutum ya ci gajiyar watan ta hanyar da ta fi dacewa.
Umarni da hani kan azumin Ramadan a takaice: Watan Ramadan Mai albarka yana daf da shigowa. Musulmi suna haba-haba da wannan wata mai girma, wanda a cikinsa suke Sallah da ambaton Allah Ta’ala suke samun alherai masu girma da lada mai yawa. Musulmi na azumtar wannan wata daga fitowar Alfijir zuwa faduwar rana ba tare da ci ko sha ko saduwa da iyali da sauransu ba.
Manzon Allah (SAW) ya ce, “Idan watan Ramadan ya kama, akan bude kofofin Aljanna a kukkule kofofin wuta kuma a daure shaidanu.” (Buhari). Wannan Hadisi na nuna cewa Ramadan watan neman gafara ne da samun albarka marar misaltuwa. Kuma kasancewar an daure shaidanu akan samu karancin barna a cikin watan. Baya ga haka an nemi Musulmi su kaurace wa abinci da abin sha da wasu ayyuka, kuma ana bukatar su aikata wasu abubuwa a cikin Ramadan.
Ga misalai daga ciki:
Abubuwan da ake so a aikata: Ya kai bawan Allah! Akwai dimbin abubuwan da Musulmi zai yi da za su sa ya amfani alheran da suke cikin watan Ramadan kamar:
Karatun Alkur’ani a kullum – Abu na farko da za ka iya yi, wanda za ka tabbatar ka samu alherai da lada mafiya girma a wannan wata mai girma, shi ne karatun Alkur’ani. A kan kowane baki na Alkur’ani akwai lada, don haka gwargwadon abin da ka karanta daga Alkur’ani gwargwadon ladan da za ka samu. Kuma yana da kyau yayin karatun ya zamo kana hadawa da sanin ma’anoninsa, domin manufar karatun Alkur’ani shi ne hakan ya taimaka maka ka zamo Musulmi nagari ba a watan Ramadan kawai ba a daukacin watannin shekaraun da za su biyo bayansa.
Sauran su ne yin sallolin nafila da sadakoki na nafila domin suna kawo lada mai yawa. Sai yin Sallar Tarawih da bayar da zakka da sada zumunta da sauran ayyukan da’a.
Abubuwan da aka hana ko ba a so a yi a cikin watan Ramadan, sun hada da kauce wa cin abincin haram da rike mutum a zuciya wato rashin yafiya ga wanda ya saba maka da rashin hakuri da aikata ayyuka na shaidanci.
Akwai kuma kura-kurai da ake son mai azumi ya kauce musu da suka hada da fushi da yawan barci a wuni da yin azumi ba tare da yin Sallah ba, da furta kalamai ba tare da aunawa ba (yawan surutu).
Manzon Allah (SAW) ya ce: “Azumi garkuwa ne (daga wuta), don haka duk wanda yake azumi ya kauce wa munanan kalamai da ayyukan jahilci. Idan wani ya zage shi ko ya neme shi da fada ya ce masa: “Ni ina azumi! Ni ina azumi!” (Buhari).
A takaice ana so Musulmi a cikin watan Ramadan ya mayar da hankali wajen neman alherai da lada mai yawa iyakar karfinsa. Kuma ya yi taka-tsantsan kan duk abin da zai yi tare da kauce wa duk abin da zai bata azuminsa ko ya hada shi gaba da mutane.
Allah Ya taimake mu mu rayu kan koyarwar Alkur’ani da Sunnah. Kuma Ya nuna mana gaskiya Ya ba mu ikon bin ta, kuma Ya nuna mana karya (da bata) Ya ba mu ikon kaurace musu.
Allah Ya kara tsira da aminci ga ManzonSa Muhammad (SAW) da alayensa da sahabbansa.
Ina kammala wannan huduba tawa ina mai rokon Allah Madaukaki Ya gafarta mana dukkan zunubanmu, ku nemi gafararSa, lallai Shi Mai gafara ne Mai jinkai.
Imam Murtada Muhammad Gusau, Babban Limamin Masallacin Juma’a na Nagazi-Ubete da ke Okene Jihar Kogi; za a iya samunsa ta: +2348038289761.