Yadda zaben Buhari ya jawo wa ‘yan kasuwar Arewa matsala
’Yan Kasuwa da suka fito daga arewacin kasar nan da ke zuwa garuruwan Legas da Anacha da Aba sayo kayayyakin ’yan kunne da bulawus da takalma da wanduna sun janye kauracewar da suka yi wa wadannan garuruwa na tsawon makonni biyu saboda musguna musu da ake yi a wadannam wuraren. ’Yan kasuwan na Arewa sun […]

’Yan Kasuwa da suka fito daga arewacin kasar nan da ke zuwa garuruwan Legas da Anacha da Aba sayo kayayyakin ’yan kunne da bulawus da takalma da wanduna sun janye kauracewar da suka yi wa wadannan garuruwa na tsawon makonni biyu saboda musguna musu da ake yi a wadannam wuraren.
’Yan kasuwan na Arewa sun kaurace wa zuwa sayo kayayyaki a wadannan garuruwa ne saboda abin da suka kira, irin gallazawar da ’yan kasuwan wadannan garuruwa suke yi masu ta hanyar kara masu farashin kudaden kayayyakin da suke sayowa da sunan tashin dala.
Da yake zantawa da waklinmu kan wannan mataki da suka dauka na janye wannan kauracewa da suka yi. Shugaban riko na kungiyar masu sayar da ’yan kunne na Arewa, Alhaji Usman Baba Sa’eed, ya bayyana cewa, babban dalilin da ya sa suka dauki wannan mataki na kauracewa zuwa Legas shi ne ana cika masu kudi a kayayyakin da suke sayowa da sunan wai dala ta tashi. “Idan muka nemi ragi sai a ce mana ba ku ne kuka zabi canji ba? Bayan haka kuma idan muka sayi kaya bayan an rubuta mana takarda, kafin mu je banki mu dawo sai a ce mana dala ta tashi, don haka za a kara mana farashi kan kayan da muka saya. Saboda haka muka umarci dukkan ’yan kasuwanmu na Arewa su kaurace wa zuwa Legas har na tsawon makonni biyu don a dauki matakin magance wadannan matsalolin.”
Alhaji Usman Baba ya yi bayanin cewa, “bayan da muka kaurace wa zuwa garin na Legas, sai muka aika masu da mutane biyar da suka fito daga jihohin Kano da Kaduna da Sakkwato da Filato da Abuja tare da wasikar koke-kokenmu, don su kai masu. Dama abin ya damu wadannan ’yan kasuwa na Legas, don haka lokacin da wadannan wakilai namu suka sauka a Legas nan take suka karbe su hanu bibbiyu kuma suka rubuta masu amsar wasikar da muka rubuta masu, tare da ba da hakuri da kuma tabbacin cewa za su dauki mataki na rage farashin kudaden kayayyakin da muke sayowa tare da daukar matakin hukumci ga duk wanda ya sake gaya mana maganar da ba ta dace ba.’’
Ya ce, don haka sun janye wannan kaurace wa zuwa Legas da suka yi, yanzu za su koma su cigaba da sayo kaya a wannan mako.
Shi ma a zantawarsa da wakilinmu, Shugaban masu sayar da bulawus a kasuwar New Market da ke garin Jos, Alhaji Abubakar Isah Muhammad, ya ce su ma a makonni biyu da suka gabata sun umarci ’yan kasuwansu da suke zuwa Anacha da Aba sayo kayayyaki su dakatar da zuwa wadannan garuruwa, saboda irin yadda ’yan kasuwan wadannan wurare suke kara masu farashi da sunan wai dala ta tashi.
Ya ce, wannan abu yana bata masu rai, don haka suka umarci ’yan kasuwansu da suke zuwa sayen kayayyaki a wadannan wurare su dakata. “Bayan mun bayar da wannan umarni mu ma sai muka rubuta masu takardar koke-kokenmu muka aika masu Anacha da Aba. Saboda takardar da muka rubuta masu sun ba mu tabbacin cewa ba za su kara yi mana irin wadannan abubuwa ba. Don haka mun janye wannan kauracewa da muka yi. Muna umartar dukkan ‘yan kasuwanmu kowa ya ci gaba da tafiya zuwa wadannan wurare don sayo kayayyaki.’’
A zantawarsa da walilinmu, Shugaban ’Yan kasuwar Takalma ta bayan banki da ke garin Jos, Alhaji Yahaya Umar, ya bayyana cewa a duk mako idan suka je Legas suka sayo kayayyaki na miliyoyin Naira. “Amma da aka samu canjin gwamnati sai ‘yan kasuwan kudancin kasar nan suka hada kai suna ta kara wa kayayyakin da suke sayarwa kudi, suna gallaza mana. Don haka mu ma muka kaurace wa zuwa sayo kayayyaki don ganin an yi gyara kan wannan matsalar.’’
Ya ce, “amma ganin suna ta kiranmu a waya suna ba mu hakuri, suna cewa sun rage farashin kayayyakinsu, mun janye wannan kauracewa, za mu tafi a wannan makon mu sayo kayayyaki.”