Yadda zaben kananan hukumomi ya gudana a Kebbi

A ranar Asabar da ta gabata ne aka gudanar da zaben kananan hukumomi a Jihar Kebbi. Wakilinmu ya na daya daga cikin tawagar manema labarai da suka zagaye kusan mafi yawan kananan hukumomin jihar, domin ganin yadda zaben ya kasance. Wakilin namu ya ruwaito mana cewar dukkan kananan hukumomin da suka ziyarta jama’a ba su […]

Yadda zaben kananan hukumomi ya gudana a Kebbi

A ranar Asabar da ta gabata ne aka gudanar da zaben kananan hukumomi a Jihar Kebbi. Wakilinmu ya na daya daga cikin tawagar manema labarai da suka zagaye kusan mafi yawan kananan hukumomin jihar, domin ganin yadda zaben ya kasance.

Wakilin namu ya ruwaito mana cewar dukkan kananan hukumomin da suka ziyarta jama’a ba su fito domin kada kuri’unsu ba, misali a kananan hukumomin Jega da Maiyama da Koko-Besse da Fakai da Danko-wasagu da kuma Sakaba, zaben tamkar ba a yi ba a yankunan, saboda kowa ka gani yana ta hidimar gabansa babu abinda ya sha masa kai.

Wadansu kananan hukumomin kuwa ‘yan siyasa sun ci karansu babu babbaka, domin wadansu rumfuna ko jami’an tsaro babu, babu kuma wakilan sauran jam’iyyu sai dai na jam’iyyar APC.

Wakilimmu ya ruwaito ma na cewar a lokacin da suka isa karamar hukumar Zuru da misalin karfe goma da rabi na safe, tuni wadansu rumfunan har sun kammala jefa kuri’u, wadansu rumfunan kuma sai dai malaman zaben zaune babu kowa, ba jami’an tsaro ba wakilan ko wace jam’iyya sai dai APC.

Yawancin kauyukan dake ketaran ruwa ba su sami kayan zabe da wuri ba, duk da yake an rarraba kayan tun ranar Alhamis, kuma dukkan kananan hukumomin da wakilinmu ya ziyarta babu inda ya ga mace ta fito domin kada kuri’anta.

Yawancin manyan jami’an gwamnatin Jihar Kebbi musamman kwamishinoni da ’yan siyasa in banda Gwamna Atiku Bagudu da mataimakinsa, Kanal Sama’ila Dabai da sakataren Gwamnatin jihar, Alhaji Babale Umar da Faruk Musa Enabo, yawancin wasu duk ba su ci rumfunan zabensu ba, jam’iyyar PDP ce ta cinye rumfunan, hatta shi kansa shugaban hukumar zaben, Alhaji Aliyu Mohammed Mera da shugaban ma’aikata na gidan Gwamnati, Sulaiman Mohammed Argungu da kakakin majalisar dokoki, Abdulmumuni Sama’ila dukkansu ba wanda jam’iyyar APC ta ci rumfarsa.

 

Wannan ya nuna cewa shekarar 2019 Gwamnoni da ’yan Majalisa na jihar da tarayya su na da gagarumin aiki. A karshe shugaban hukumar zabe mai zaman kanta na jihar, Alhaji Aliyu Mohammed Mera ya Shaidawa ’yan jarida cewa APC ta cinye dukkanin kujerun shugabannin kananan hukumomi 21 dake jihar Kebbi, amma har lokacin da na hada wannan rahoto ba su bada sakamakon zaben dukkanin kansiloli na kananan hukumomin ba.