Yadda zaben Saliyo karo na faro ya gudana

Shugaban ’yan adawar kasar Saliyo Julius Maada Bio ya lashe zaben Shugaban kasar da aka gudanar a zagayen farko na zaben Shugaban kasa da aka yi a Saliyo. Mista Maada Bio, ya lashe kashi 43 cikin 100 na kuri’un da aka kada, inda ya yi nasara a kan abokin takararsa Samura Kamara na Jam’iyyar All […]

Yadda zaben Saliyo karo na faro ya gudana

Shugaban ’yan adawar kasar Saliyo Julius Maada Bio ya lashe zaben Shugaban kasar da aka gudanar a zagayen farko na zaben Shugaban kasa da aka yi a Saliyo.

Mista Maada Bio, ya lashe kashi 43 cikin 100 na kuri’un da aka kada, inda ya yi nasara a kan abokin takararsa Samura Kamara na Jam’iyyar All Peoples Congress da kashi daya rak kamar yadda BBC ta rairayo sakamakon zaben.

Shi dai Maad ya taba jagorantar Saliyo a lokacin mulkin soja a 1996.

Kuma nan da mako biyu mutanen biyu za su sake karawa a zagaye na biyu na zaben inda za a fitar da sakamakon karshe na wanda zai ci gaba da jan ragamar kasar.

Shugaba Ernest Bai Koroma zai sauka daga mukamin Shugaban Saliyo ne bayan shafe shekara 10 yana karagar mulki.