Yadda zaman kwamitin ba da shawarwari kan fina-finan Najeriya ya gudana a Jos

Kwamiti ba da shawarwari kan fina-finan Najeriya da suka hada da na Hausa da na Turanci da Yarabanci da Ibo da sauransu sun yi zama a garin Jos, Jihar Filato don ba da shawarwarin yadda za a inganta harkar fim a Najeriya.Taron da aka dauki kwana biyu ana gudanar da shi an tattauna matsalolin da […]

Yadda zaman kwamitin ba da shawarwari kan fina-finan Najeriya ya gudana a Jos
Yadda zaman kwamitin ba da shawarwari kan fina-finan Najeriya ya gudana a Jos

Kwamiti ba da shawarwari kan fina-finan Najeriya da suka hada da na Hausa da na Turanci da Yarabanci da Ibo da sauransu sun yi zama a garin Jos, Jihar Filato don ba da shawarwarin yadda za a inganta harkar fim a Najeriya.
Taron da aka dauki kwana biyu ana gudanar da shi an tattauna matsalolin da suka yi cacukwi da masana’antun shirya fina-finai da kuma yadda za a shawo kansu.
Matsalolin da aka bayyana sun hada da karancin kudi da satar fasaha da rashin ingancin labarai da karanci kayan aiki da sauransu.
Wannan shi ne taro na farko tun bayan lokacin da Hukumar Kula da Shirya Fina-finan Najeriya (Nigeria Film Corporation NFC) ta kafa kwamitin ba da shawarwarin wata daya da ya wuce.
A lokacin da Shugaban Hukumar NFC Dokta danjuma Dadu yake jawabi a wurin taron ne ya ce an kafa wannan kwamitin ne don ganin an ciyar da harkar fim gaba a Najeriya.
Ya ce, Bayan ya zama shugaban hukumar ne a watan Mayun wannan shekarar ne ya kai ziyara ga masu ruwa da tsaki a harkar shirya fina-finai na Najeriya da suka hada da Arewaci da Kudanci da kuma Gabashi, ya samu korafe-korafe a kan karancin kudi da muhalli da kwarewa da kasuwanci da dillanci da wuraren shirya fina-finai da sauransu.
A karshe ya yaba wa mambobin kwamiti bisa kwazo da kuma hadin kan da suka bayar.
Shugaban kwamitin Mista Brendan Shehu ya yaba wa hukumar NFC bisa kafa kwamitin ba da shawarwarin, ya kuma ce za su yi iya bakin kokarinsu wurin ciyar da harkar fim gaba.
Kwamitin yana kunshe da mutum 13 da suka hada da Mista Brendan Shehu (Shugaba), Cif Tunde Oyelede da Mista Mahmood Ali Bologun da Cif Pete Edochie da Mista bictor Okhai da Cif Osita Okeke (Ossy Affason) da Prince Chuwang R. Pam da Mista Yakubu Jang da Alhaji Sani Mu’azu da Misis Lantana Ahmed da Misis Hanatu Dantong da Alhaji Ahmed dahiru Beli Daraktan Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano da kuma  Mista Gideon Barde.