Yadda Zamfarawa suka yi addu’o’in neman zaman lafiya

Al’ummar Zamfara sun gudanar da addu’o’i na musamman a fadin jihar domin samun cikakken tsaro da zaman lafiya

Yadda Zamfarawa suka yi addu’o’in neman zaman lafiya

Al’ummar Zamfara sun fito kwansu da kwarkwata domin gudanar da addu’o’i na musamman a fadin jihar domin samun cikakken tsaro da zaman lafiya.

Sarkin Dansadau, Alhaji Abubakar Muhammad S Kudu na daga cikin daruruwan mutane da suka halarci addu’ar da aka gudanar filin sallar ido da ke  Gusau, babban birnin jihar.

An gudanar irin wannan taron addu’a a lokaci guda a ɗaukacin kananan hukumomin jihar domin samun sauki daga ayyukan ’yan bindiga da suka addabi al’ummar jihar.

Malaman addini da dalibai da jami’an gwamnati da sauran jama’a na halartar taron addu’ar ta musamman inda ake ta sauke alkur’ani da kuma sallah da neman dauki daga wajen Allah.

Sarkin Dansadau, Alhaji Abubakar Muhammad S. Kudu, ya shaida wa wakilinmu cewa taɓarɓarewar tsaro a jihar ce ta sa manya suka ga ya dace a koma ga Allah a nemi taimakonSa kan sha’anin tsaro a jihar.

 

“Mu al’ummar Dansadau ba ma iya barci da idanunmu biyu a rufe saboda fargabar harin ’yan bindiga.

“Tsananin abin ya kai yadda idan mutum ya kai dare, ba sa tunanin ko za sun wayi gari lafiya.

 

“Lamarin ya fi muni a yankunanmu be saboda muna makwabtaka da jihohin Neja da Kaduna da kuma babban jerin da ’yan ta’adda suka mayar matattararsu,” in ji basaraken.