Yadda ziyarar bin Salman ta wakana a Amurka

Shugaban kasar Amurka Donald Trump da Yariman Saudiya Mohammed bin Salman sun tattauna a kan abubuwa da suka shafi harkar tsaro da kasuwanci da hadin kai a lokacin da Yariman ya kai ziyara Fadar White House. Da yake bayani a kan sauye-sauye da kasar Saudiya ke fuskanta a ’yan kwanakin a karkashin jagorancin Bin Salman, […]

Yadda ziyarar bin Salman ta wakana a Amurka

Shugaban kasar Amurka Donald Trump da Yariman Saudiya Mohammed bin Salman sun tattauna a kan abubuwa da suka shafi harkar tsaro da kasuwanci da hadin kai a lokacin da Yariman ya kai ziyara Fadar White House.

Da yake bayani a kan sauye-sauye da kasar Saudiya ke fuskanta a ’yan kwanakin a karkashin jagorancin Bin Salman, Mista Trump ya yaba wa Yariman bisa namijin kokarin da yake yi, “Yanzu abubawa sun fi tafiya daidai, kuma ina tunanin cewa za su ci gaba da tafiya yadda ya kamata. An bunkasa harkar kasuwanci a kasar Saudiyya, wanda hakan ke nufin cewa mutanen kasar za su samu aiki,” inji Trump kamar yadda ya shaida wa manema labarai bayan sun kammala tattaunawa.

Shugaban Trump ya nuna wani hoto da ke nuni da wasu manyan makamai da kasar Saudiyya za su saya wadanda suka hada da jiragen yaki da makaman kare dangi da motocin yaki.

“Saudiyya kasa ce mai arzikin gaske, kuma muna sa ran cewa za ta lasa wa kasar Amurka kadan daga cikin wannan arzikin, watakila ta hanyar samar da ayyukan yi sayen makamai a ko’ina a duniya,” inji shi.

A nasa bangaren, Yariman Mohammed bin Salman wanda Trump ya girma da shekara 39, ya nuna tarihin alaka tsakanin kasashen biyu.

“Mu ne tsofaffin kawayen Amurka a yankin Larabawa, saboda mun kwashe sama da shekara 80 muna alaka a bangarorin siyasa da tsaro da tattalin arziki. Yadda assasa wannan alakar ke da matukar karfi da tarihi,” inji shi.

A bara, shugabannin biyu sun amince da tsarin kashe kimanin  Dala biliyan 200 wanda ya hada da sayen makamai daga Amurka. Amma kuma bayan ziyarar, Bin Salman ya ce tsarin da suke yi ya wuce haka, kasuwancin da suke shirin yi a tsakaninsu yana da yawa.

“Kamar yadda ka sani ne Mai girma Shugaban kasa, tunda ka zama Shugaban kasa, mun tsara cewa za mu yi harkar kasuwanci na Dala biliyan 200 a cikin shekara hudu, amma sai ya koma Dala biliyan 400 saboda samun dama,” inji Bin Salman.