Yadda ziyarar Osinbajo  Kasuwar Alabar Rago ta haifar mana alheri –Nagogo

Alhaji Umar Nagogo Sakkwato, shi ne Sarkin Kasuwar Duniya ta Alabar Rago a Legas, ya jinjina wa Gwamnatin Tarayya da ta sanya su cikin jerin takwarorinsu da suka karbi tallafin kudi domin bunkasa harkokin kasuwancinsu. Sarkin Kasuwar ya yi wannan jinjina ce a hira da Aminiya jim kadan bayan ziyarar Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi […]

Yadda ziyarar Osinbajo  Kasuwar Alabar Rago ta haifar mana alheri –Nagogo

Sarkin Kasuwar Alabar Rago, Alhaji Umaru Nagogo Sakkwato

Alhaji Umar Nagogo Sakkwato, shi ne Sarkin Kasuwar Duniya ta Alabar Rago a Legas, ya jinjina wa Gwamnatin Tarayya da ta sanya su cikin jerin takwarorinsu da suka karbi tallafin kudi domin bunkasa harkokin kasuwancinsu. Sarkin Kasuwar ya yi wannan jinjina ce a hira da Aminiya jim kadan bayan ziyarar Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osibanjo wanda ya raba tallafin ga kananan ‘yan kasuwar:

 

Aminiya: Me Mataimakin Shugaban Kasa ya zo muku da shi a wannan ziyara?

Sarkin Kasuwa: Muhimmin abu na farko shi ne, wannan ziyara da Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya kawo zuwa Kasuwar Duniya ta Alabar Rago ita ce ta farko da wani babban jami’in Gwamnatin Tarayya ya taba kawowa a tarihin kasuwar. Duka inda ba ka zaci zai sa kafarsa ba ya je ya gane wa idanunsa irin zaman da muke yi.

Abu na biyu shi ne, kamar yadda ya kai irin wannan ziyara a wasu sassan kasar nan, mu ma ya zo mana da irin wannan tallafi da gwamnati take bayarwa ga kananan ’yan kasuwa. An yi wa irin wadannan kananan ’yan kasuwa su fiye da miliyan 1 rajista wanda a nan take tun kafin ya kammala   ziyarar wadansu daga cikinsu suka fara ganin sakon shigar kudin cikin asusunsu na banki. Wannan hobbasa da Gwamnatin Tarayya a karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi mana, babu abin da za mu ce sai fatan Allah Ya saka musu da alheri, Ya yi musu jagoranci.

Aminiya: Masu hamayya suna sukar wannan tsari cewa ana bayar da tallafin ne domin sayen jama’a saboda zaben da ke tafe. Me za ka ce a kan haka?

Sarkin Kasuwa: Wallahi wannan ba gaskiya ba ce, domin nuna hamayya bai dace wani ya wuce gona da iri ba. Ina so in fayyace maka cewa, mu ’yan kasuwa ne babu ruwanmu da siyasa. Irin wannan tallafi muke bukata domin idan karamin dan kasuwa ya samu irin wannan tallafi to zai yi farin cikin da bai taba yin irinsa a rayuwa ba. A nan cikin Kasuwar Alaba akwai kananan ’yan kasuwa masu saro kwarya daya ta lemun zaki a kan Naira 1,500 da masu sayen kwandon tumatir a kan Naira dubu 4 suna kasawa a kan hanya suna sayarwa ga jama’a. Akwai masu sayar da muruci da rake da ayaba da abarba da kankana da kayan gwari da kayan abinci iri-iri da sauran kayan bukatun yau da kullum da suka dogara da dan abin da suke samun riba don ciyar da kansu da iyalansu. Wallahi masu sukar wannan tsari ba su yi wa kananan ’yan kasuwa adalci ba! Wato ke nan suna so a kyale mutane kara-zube cikin kuncin rayuwa da zai haifar da karuwar miyagun ayyuka a kasa.

Aminiya: Kananan ’yan kasuwa nawa ne suka fara karbar tallafin a ranar?

Sarkin Kasuwa: Ni da kaina na tabbatar da mutum 500 da suka karbi tallafin a ranar, saura kuma sun ci gaba da samun nasu daga baya. Kimanin mutum miliyan 1 aka yi wa rajista wadanda mun sani cewa ba duka za su samu ba.

Aminiya: Me ya sa kake ta yabon wannan ziyara ta Mataimakin Shugaban Kasa?

Sarkin Kasuwa: Ai yabon gwani ya zama dole, saboda ganin wannan kasuwa bangare uku ce, akwai sashen Alaba International da kabilun Ibo a ciki da sashen Jakara wato Karambosuwa na Yarbawa da sashen Alabar Rago ta Hausawa. Amma duka Mataimakin Shugaban Kasa ya tsallake su ya zo bangarenmu kuma ya ba mu wannan tallafi wanda shi da kansa ya tabbatar cewa tallafin zai yi mana amfani. Ka ga ai ya zama wajibi mu jinjina wa Gwamnatin Baba Buhari.

Aminiya: Yaya zamantakewar mutanenka da sauran kabilu a kasuwar?

Sarkin Kasuwa: A gaskiya akwai kyakkyawar zamantakewa tsakaninmu da ’yan uwanmu da muke yin komai tare. Muna tare da su tsakani da Allah da zamantakewar girma da arziki. Ba mu taba kwance musu zane ba, haka su ma ba su kwance mana. Fahimtar juna a tsakaninmu da su ne ta sa ka ji shiru ba ka jin rigingimu ko fitina a tsakaninmu. Hakan ya biyo bayan  nada shugabannin sassa daban-daban na kasuwar da muka yi ne inda muke zama bisa teburi daya a kullum domin tattaunawa kan yadda za mu shawo kan matsalolin da muke fuskanta domin ci gabanmu baki daya. Kuma da kanmu muke ladabtar da mutanen da suka aikata wasu laifuffuka bisa kwatanta gaskiya da adalci. Abin da ya gagare mu sai mu mika shi ga jami’an tsaro domin akwai kyakkyawar dangantaka a tsakaninmu da su.

Aminiya: Me za ka ce a kan kiraye-kirayen mahukunta kan zama lafiya a Legas da kasa baki daya?

Sarkin Kasuwa: Wannan muhimmin abu ne kwarai domin sai da zaman lafiya ake samun ci gaba. An ce a bi Allah a tsira, a bi hukuma a zauna lafiya. Ni ina goyon baya dari bisa dari cewa dukan mutumin da ya san yana da matsala tsakaninsa da hukuma to ya je ya gyara zamantakewarsa da su domin hukuma ita ce zaman lafiyarmu, duk inda babu hukuma to ba zaman lafiya a wannan wuri. Alheri da ci gaba ba sa samuwa a wurin da ba zaman lafiya.

Aminiya: A karshe wane kira za ka yi wa jama’a a irin wannan lokaci?

Sarkin Kasuwa: Kiran da nake yi ga jama’a bai wuce su yi hakuri su zauna da lafiya da abokan zamanasu ba. Sannan ga zaben kasa ya zo kusa, to lallai ne mu tsaya mu lura da kyau wajen zaben mutanen kirki masu kishin kasa da son ci gabanta a kan mukamai. Kada mu yarda a yi mana sakiyar da ba ruwa wajen sayen katin zabe. Kuri’arka ita ce hujjarka domin idan ka kuskura ka sayar da katin zabenka, to ka zubar da mutuncinka ba ka da ta cewa a rayuwarka.