Yadda’yan zuri’a guda ke mutuwa ranar 2 ga Fabrairun kowace shekara

An dauki kimanin shekaru hudu ke nan da ahalin wata zuri’a a kasar Indiya ke mutuwa da zarar 2 ga watan Fabrairun shekara ya zagayo. Don haka iyalan wannan zuri’a ke zaman dar-dar da farhgabar ranar 2 ga Fabrairun kowace shekara. Pokhan Ram, mazaunin kauyen  Lakhanipur-Maheshpatti a gundumar Samastipur da ke da nisan kimoita 90 […]

Yadda’yan zuri’a guda ke mutuwa ranar 2 ga Fabrairun kowace shekara

An dauki kimanin shekaru hudu ke nan da ahalin wata zuri’a a kasar Indiya ke mutuwa da zarar 2 ga watan Fabrairun shekara ya zagayo. Don haka iyalan wannan zuri’a ke zaman dar-dar da farhgabar ranar 2 ga Fabrairun kowace shekara.

Pokhan Ram, mazaunin kauyen  Lakhanipur-Maheshpatti a gundumar Samastipur da ke da nisan kimoita 90 a gabashin Patna. ’Yan uwan Ram sun mutu a hadarin mota ranar 2 ga Fabrairun 2015. Wadannan iyalai sun yi makoki, duk da haka suka dauka wata kaddara ce daga Ubangiji, sai suka ci gaba da sha’anin rayuwarsu.

Kwatsam cikin shekarar 2016, ranar 2 ga Fabrairu sai dan uwansa Bechan Ram mai shekara 30, wanda ya kasance na biyu a jerin ’yan uwan da suka mutu. Sai wani mummunan abin alhinin ya sake far musu cikin shekarar 2017, inda yayansa, wato Fekan Ram mai shekjara 35 ya mutu.

Kuma ranar 2 ga Fabrairun bana (2018) sai mahaifinsa Sakhindra Ram mai shekara 60 ya mutu. “Ba mu san kan wanda za ta kewaya ba a shekara mai zuwa,” inji Pokhan, wanda ya yi bayani cikin karkarwar murya.

Mutanen kauyen suna cike da mamaki faruwar wannan lamari na musamman. “Lamarin na da daure kai, amma dai shi ne hakikanin gaskiya,” a cewar shugaban kauyen Benazir Bano..

Shi kuwa wani wakilin jama’a a majalisar mulkin kauyen, Yogendra Singh ya ce lamarin haka akwai yake faruwa daidai wanan lokacin (dace ne kawai).