Yadudu da Kukah na dari-dari da taron kasa da za a yi

Farfesa Auwalu Yadudu da Bishop Mathew Hassan Kukah mutane ne da suka halarci tarurrukan gyaran tsarin mulki a lokuta daban-daban, saboda haka ne Aminiya ta tuntube su domin jin ta bakinsu game da taron kasa da za a gudanar kwanan nan , inda dukkansu suka nuna shakku game da samun kyakkyawan sakamako daga taron. Ga […]

Yadudu da Kukah na dari-dari da taron kasa da za a yi

Farfesa Auwalu Yadudu da Bishop Mathew Hassan Kukah mutane ne da suka halarci tarurrukan gyaran tsarin mulki a lokuta daban-daban, saboda haka ne Aminiya ta tuntube su domin jin ta bakinsu game da taron kasa da za a gudanar kwanan nan , inda dukkansu suka nuna shakku game da samun kyakkyawan sakamako daga taron. Ga yadda hirar ta kasance:

Zai yi wuya taron ya fitar da abin kirki -Farfesa Yadudu

Aminiya ta samu tattaunawa da Farfesa Auwalu Yadudu, baban malamin jami’a kuma masanin shari’a wanda ya yi bayanai a kan taron kasa da kuma makomar taron. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Isa Muhammad Inuwa, daga Kano

Aminiya: Farfesa wane muhimmanci kake jin wannan taron yake da shi kuma meye amfaninsa ga Najeriya da kuma ‘yan Najeriya?
Yadudu: Ita maganar jama’a su taru su tattuna wadansu muhimman abubuwa game da makomar kasa ba aibu ba ne kuma ma abin da za a so ne. Kuma shi tsari na dimukuradiyya haka yake so, amma shi wannan taro ba irin wannan ba ne. Taro ne kawai na dare daya, kamar mafarki aka yi, ba shi da wata manufa cikakkiya, tsayayyiya wadda za ka ce irin waccan ce.
Abin da ya sa  na fadi haka shi ne, su dai wadanda suka kawo wannan lamarin kamar kawai cikin dare daya suka tashi suka yi wannan tunanin,  domin shi shgaban kasa a farkon hawansa akwai wadanda suka tasa shi a gaba da kuma koke-koke da ake yi na cewa a gudanar da taron kasa mai cin gashin kansa, kuma kabilu ne za su aiko da wakilai. Amma sai ya tirje, ya shure ya ce shi yana ganin babu wani taro da za a yi a kasar nan wanda ake bukata a yi, wanda ba a taba yi ba.
Ya ce abin da ya rage shi ne a tattara bayanai na tarurrukan da aka yi a baya a fitar da wata matsaya. To sai a yi mamaki kuma cewa mene ne ya sa dare daya ya canja ra’ayinsa idan ba kawai wata manufa ce wacce take ba a fitar da ita a bayyane ba, sai dai kawai da dungu aka kawo maganar.
Aminiya: Za a iya fadar hakan ganin cewa zabe yana tafe kuma ana tunanin shugaban kasa zai sake tsaywa?
Yadudu: To a gaskiya za a iya kallon abin ta haka, amma abin damuwa shi ne, shi wannan taro ba shi ne zai karfafa ko raunana tsayawarsa ba. Amma kuma akwai abubuwa na dar-dar na shi taron yadda aka shirya shi da manufarsa da kuma takidin da ake yi.
Za a iya samun wadansu abubuwa su taso wadanda suke ba masu kyau ba su dagula ruwa kuma zaben ma ya zamana a samu hujjar cewa ko ba za a yi ba, ko kuma a yi wata dabara wadda take za a ce ga jama’a an tara kuma su suka ce a yi haka, ko kada a yi haka.
Aminiya: Wai shin ma taron ya dace a yi shi a yanzu?
Yadudu: Fisabilillahi a bisa dukkan alkaluman da ake gani, sai ka yi mamaki wane irin taro ne za ka yi wanda zai fitar da wadansu shawarwari da za su samu karbuwa har a yi wata doka ko kuma a sake lalen shi kundin tsarin mulki kuma a yi aiki da shi kafin zabe? Wannan  ba zai yiwu ba. Saboda haka nake ganin cewa da a ce za a yi shi yanzu da kuma tafarkin da aka dauko na yin sa, sai ka ga cewa manufar ba ta a yi taron ba ne, kawai dai ana hangen da wadanne hanyoyi ne mahukunta daga sun shiga wani runtsi za su bi  su samo madogara ta karfafa yardar jama’a gare su da kuma hanyoyin da idan abu ya dagule za su iya ci gaba da mulki ko da an yi zabe ko ba a yi zabe ba? Akwai wannan tsoron cewa wannan lokaci bai dace ba, kuma idan ma aka duba yadda doka ta tanada, za a iya cewa ma ba zai yiwu ba.
Aminiya: Kana ganin taron zai iya jawowa a yi wa kundin tsarin mulkin kasa wani gyara ko wata kwaskwarima?
Yadudu: To tunda kamar yadda suka ce ana iya tattauna komai ban da batun wargajewar kasa, to ai ka ga za a iya kawo shawarwari da yawa da suke sun shafi wani tanadi . Za su iya cewa a canja tsarin shugaba ba mai cikakken iko a koma wani tsari. Za su iya cewa maimakon shekara hudu a koma biyar ko shida ko ma nawa ne. Za su iya cewa ma a yi watsi da tsari na jihohi a koma tsarin shiyya-shiyya.
To ka ga idan sun kawo wannan shawara, duk da dai su mahukunta sun ce kowace shawara aka kawo sai an mika ta ga majalisar kasa, sannan ne za a ga wannan shawarar da suka kawo za ta samu karbuwa kuma a canja kundin tsarin mulki. Domin ba za ka iya canja kundin tsarin mulki a kasar nan ba a yanzu, idan ba ka bi ta tanade tanaden da ya yi ba, shi kansa. Wannan hanyar da suka biyo kuwa ba zai yiwu ba.
Aminiya: Zaben wakilan da za su tattauna, nada su ya kamata a yi ko kuwa mutane ne ya kamata su zabe su?
Yadudu: Ai kwamitin da suka kafa ya jiyo ra’a yin jama’a na yaya za a yi abin, shawarar da ya ba su karara ce, jama’a a kasar nan sun gaji da irin wannan nade-nade da ake yi na son zuciya domin wadanda za su zo ne su gabatar da abin da mahukunta suke so su ji ko da bai dace ba. Kamata ya yi wakilan su zamana zababbu ne kuma zaben ya zama an yi shi shi a bisa tsarin da doka ta wakilci da kuma kundin tsarin mulki suka tanada.
Aminiya: Me kake ganin taron zai iya haifarwa daga karshe?
Yadudu: A bisa sanina na yadda ake yin wadannan tarurruka, kuma na shiga irin wadannan tarurruka tun daga wajen shekara talatin zuw yau, bana ganin akwai wani kyakkyawan sakamako da wannan taro zai fitar da shi. Babu lokaci, babu kyakkyawar niyya, sannan babu tanadi kyakkyawa. Abin tsoro shi ne, kada a yi mamakin cewa za a yi amfani da wannan dandali ne a tsokano wadansu rigingimun da za su raba kan jama’a kuma raba kan jama’ar nan don wani ya samu burin daukaka ta siyasar da yake da ita. Ko ya zamana raba kan jama’ar da aka yi ya wuce yadda shi wanda ya tsokano wannan fada yake nufi, ya zamana zaben da za a yi ya zamo tashin hankali da tarzoma da fada da juna da kace- nace da za a yi su hana ma a yi zaben. Shi ya sa duk wadanda suke cewa wannan lokacin bai dace ba, wannan suke gani.

 

Siyasa kawai za a yi a wurin taron kasa – Bishop Kukah

Bishop Mathew Hassan KukahBishop Mathew Hassan Kukah, sanannen dan gwagwarmaya ne kuma Sakataren Kwamitin Gyaran Tsarin Mulki a lokacin mulkin Cif Olusegun Obasanjo. Shi ne Bishop din darikar Katolika na Sakkwato, a zantawarsa da Sashin Hausa na BBC, ya ce babu abin da zai gudana a wurin taron kasa face siyasa da neman magoya baya a tsakanin manyan jam’iyyun siyasar kasar nan wato PDP da APC:

Daga Nasiru Bello, Sakkwato

Aminiya: Nan gaba kadan a kasar nan za a gudanar da Taronn kasa ko yaya kake kallon lamarin?
Da farko dai duk abin da za a yi don ci gaban Najeriya muna na’am da shi, in mun duba abubuwan da ake ciki a Najeriya za mu iya cewa ’yan siyasar Najeriya ba su daraja siyasa ba, don haka har yanzu talakawa suna cikin wahala. Domin ba a nuna an damu da rayuwar talakawan ba, sun nuna abin da kawai suke bukata mulki, mulki, mulki! Wannan taron tunda Allah Ya sa na halarci irinsa ba sau daya ba, damuwata ba zaman makomar kasa ba, ko na yadda za a zabi wakilan al’umma a zaman ba.
Na farko ’yan siyasa ne za su wakilci kansu da kansu. Tun daga Shugaban kasa har zuwa gwamnonin jihohi ba wanda zai zabi mutumin kirki kwararren dan Najeriya da talakawa suke so, in shugaba ko gwamna ba ya sonsa wannan shi ne farkon targaden da za mu samu.
Na biyu ’yan siyasa za su tafi Abuja su yi irin abin da suka saba yi, kuma in mun dubi abin da ake ciki yanzu irin hayaniyar da ake ciki ba mu san gaba da baya ba, wato abin da ke faruwa a jam’iyyun siyasa a APC da PDP da sauransu, a ganina abubuwan da ake gani a waje su za a aikata a Abuja a gama kowa ya kama hanya ya koma gida matsololin Najeriya na nan ba gaba ba baya sun tsaya cik.
Aminiya: Wace hanya za a bi wajen zaben mutanen da za su tafi taron?
Ka san ni damuwata ita ce ba wai sai da taron kasa ne za mu samu wutar lantarki da tsaro da ruwa da hanya ba, ba sai an yi shi ne talakawa za su samu rayuwa (mai kyau) ba, abubuwan da ke damunmu kowa ya sani, kuma kasa na da tabbataccen arzikin da Allah Ya yi mata, amma har yanzu ga wulakanci da yunwa abubuwan da ke damun mutanen kasar nan ke nan. A ganina wannan taro ’yan siyasa ne za su je su yi taronsu domin wannan shekarar zabe ce, in mun ci gaba da yadda ake tafiya da kyar za a yi zabe lafiya, kodayake gwamnati ta ce wata uku ne, gaskiyar magana ba za a iya gama wannan taro cikin wata uku ba. Kwamitin Oputa, Shugaban kasa ya ba mu wata uku mu yi shi, shekara biyu muka yi, gyaran lamurran zabe a kasar nan Shugaban kasa ya ba mu wata biyu, muka yi kusan wata bakwai na san ko yaya aka yi, ba za a iya wannan taron cikin wata uku ba.
Aminiya: Me za ka ce kan maganar da shugaban taron ya yi cewa ’yan Najeriya ne za su zabar wa kansu makomar da suke son kasar ta kasance?
In ka tambayi dan Najeriya zai ce maka aiki yake nema don ya sha wahala, iyayensa sun sha wahala a lokacin da yaransu ke makarantu sun gama babu aikin yi.  Mutanen kasar nan suna cikin wahala iri-iri idan aka ce mutane su zabi wadanda za su iya fadin abin da ke damunsu za mu iya cewa za a yi taron kirki. Dubi yadda aka shirya komai da komai Shugaban kasa zai zabo wakilan taron da gwamnoni a karshe in an zo fadin me mutanen kasar nan suke so ba za a samu cikin wadannan wakilai ba.
Aminiya: A cikin wakilai fiye da 400, Shugaban kasa za a ba shi wakilai 100 ne ba ka ganin wannan ba zai sa a yi yadda ake so ba tunda an samu cudanyar mutanen da wadada ba na gwamnati ba?
Mutane kusan 500 za a tara, yawacin mutanen nan ba su san juna ba, ba su taba ganin juna ba. Saboda haka da zarar an taru ’yan APC za su fara neman mutanensu haka ma PDP, abin da zai faru ke nan a karshe kawai za a tattauna rayuwar APC da PDP ne. Damuwata kawai za a kashe kudi a banza daga karshe rahoton ma da wuya gwamnati ta samu aiwatar da abin da zai fito. Mun san abubuwan da ke damunmu, ba dan Najeriya da in ka tambaye shi ba zai iya fada maka abin da ke damunsa ba, ’yan siyasa sun san abubuwan da ke damunmu, amma ba su samu karfin halin da za su magance mana ba. Da ’yan siyasa sun hada kai, da su magance mana wadannan kashe-kashe da muke fama da su amma ina, mulki kawai suka sanya a gaba koda mene ne mai mulki ba ya son ya sauka, ai ya kamata mu tambayi kanmu shekara hudu da suka wuce me ya canja? Amma ina sai dai maganar mulki, a ganina in an fara taron makomar kasa daga yau har zuwa shekara miliyan Najeriya ba za ta canja ba, in ba ’yan siyasar Najeriya suka canja zukatansu ba. Allah dai Ya sa a gama lafiya amma ban ba da gaskiya ba a ce abubuwan da za a samu sulhu a kasar nan sai da taron kasa za a iya samunsu. Ko barawo yana bukatar zaman lafiya to yanzu akwai zaman lafiyar? Namu taron kasar da aka yi akwai abubuwa da dama da suka fito amma yanzu ina suke? A karshe yaya aka yi?  An ce in sun kammala cacar bakinsu za a kai zauren majalisun tarayya, kuma muna ganin abubuwan da ke faruwa yanzu. Naira biliyan bakwai da aka ce za a kashe don gudanar da taron a matsayin asara ce kawai. Shata ya ce, ‘kudi a kashe su ta hanya mai kyau.’ Bisa ga yadda ake ciki a kasar nan Naira biliyan bakwai na matsayin kudin caca. Da kasar Ghana ce ko Nijar ko Chadi da sun san abin da za su yi don manyan kudi ne, amma a rayuwar Najeriya Naira miliyan dubu bakwai ba wani abu ba ne. Amma ya kamata a sani akwai wasu abubuwa da kudi ba za su saye ba kamar aminci, don haka matsalarmu a kasar nan ba maganar kudi ne ba, duk wani abu da za a yi sai ka ga kowa yana kallon kudi ba niyya da tsoron Allah da kishin kasa ba.