Yaga katin PDP da Obasanjo ya yi ya dace?

A kwanakin baya ne tsohon Shugaban kasa, Janar Olusegun Obasanjo ya yaga katinsa na jam’iyyar PDP, inda ya sanar da cewa ya fita daga jam’iyyar. Abin tambaya a nan shi ne, shin matakin da ya dauka na yaga katin, ko ya dace? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga jama’a: Matakin da ya dauka […]

Yaga katin PDP da Obasanjo ya yi ya dace?
Yaga katin PDP da Obasanjo ya yi ya dace?

A kwanakin baya ne tsohon Shugaban kasa, Janar Olusegun Obasanjo ya yaga katinsa na jam’iyyar PDP, inda ya sanar da cewa ya fita daga jam’iyyar. Abin tambaya a nan shi ne, shin matakin da ya dauka na yaga katin, ko ya dace? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga jama’a:

Matakin da ya dauka bai dace ba – Baffa Disina

Hamza Aliyu,a Bauchi

Baffa Haruna Disina: “Abin da tsohon Shugaban kasa Obasanjo ya yi, gaskiyar magana bai dace ba; domin yana gidan kurkuku aka fito da shi, aka ba shi tikitin takara amma saboda wasu dalilai na son zuciya ya fice daga gidansu. PDP ta taimaki Obasanjo shi ma ya taimake ta amma saboda ba a damawa da shi a Gwamnatin Tarayya sannan babu yaransa a cikin gwamnatin, wadanda suke rike da mukaman ministoci.
“Abin da ya kamata ya yi shi ne, ya kira shugabannin jam’iyyar ya ba su shawarwarin da yake ganin idan an dauka abubuwa za su daidaita. Kowa ya san cewa Shugaba Jonathan yaron Obasanjo ne kuma shi ne wanda ya fara tallata shi a Najeriya. Siyasar ubangida ita ce ta lalata dimokuradiyyar Najeriya amma ina tabbatar wa al’umma cewa za a samu sauyi, domin yanzu kan mutane ya fara wayewa.”

Yaga katin da ya yi kuskure ne – Dokta Chindo Ilela

Hamza Aliyu, a Bauchi

Dokta Muhammad Chindo Ilela: “A fahimta ta, duk Najeriya babu wani mutum wanda ya amfana da mulkin dimokuradiyya kamar Obasanjo, domin kowa ya san cewa PDP ta yi masa riga da wando, sannan shi ma ya tallafa wa PDP amma saboda wasu matsaloli na cikin gida sai ga shi yau yana cewa shi da PDP har abada. Shi ya fi kowa sanin dokokin PDP kuma a gani na har yanzu yana cikin jam’iyyar bai fita ba.
“Akwai tsarin da ake bi idan mutum yana so ya fice jam’iyyarsa. Kowa ya san cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba da dama wa mutum ya shiga duk jam’iyyar da yake so. PDP ta yi komai wa Obasanjo, ita ta wanke shi ya zamo da a cikin al’umma. Watakila allurarsa ta soja ce ta tashi, don haka ya ga ya kamata ya yaga katin, ya nuna wa duniya.”

Yaga katin bai yi daidai ba – Tanimu Katsina

Ahmad Kabir, a Katsina

Alhaji Tanimu Katsina: “A gani na, Obasanjo bai yi daidai ba keta katin da ya yi. A matsayinsa na babba kuma uba, wanda ake ji da shi a siyasance a Najeirya baki daya, bai kamata a ce ya yi haka ba a bainar jama’a. Ya nuna cin fuska ne ga jam’iya. Bai yi tunanin wata rana zai dawo mata ba? Ai jam’iyar PDP ce ta kawo shi matsayin da yake ciki har yanzu.

Matakin Obasanjo ya yi daidai – Rabe Kafinta

Ahmad Kabir, a Katsina

Alhaji Rabe Kafinta: “Obasanjo ya yi daidai saboda lokacin da ya ce ya shiga PDP, ai takarda aka rubuta kuma har ya ba da hotonsa. To kasancewarsa na dattijo bai kamata a ce ya ga mafita a wajensa ba kuma a ce kada ya bi wannan mafita. A ce a ba shi hakuri, ai a baya can ba hakurin aka ba shi ba ya zo. Dacewa ta sa ya shiga jam’iyar kuma wannan dacewar ya hango ya fita.”

Matakin Obasanjo ya dace – Auwalu Azare

Abubakar Haruna, a Legas

Auwalu Azare: “Abin da Shugaba Obasanjo ya yi na yaga katin PDP ya dace saboda ya nuna musu fushinsa ne a fili, ba tare da wani boye-boye ba saboda ya bi su amma suka ki saurarensa, ka ga ko waye matakin da ya kamata ya dauka ke nan.”

Obasanjo ya yi daidai – Rabi’u Yunusa

Abubakar Haruna, a Legas

Rabi’u Yunusa: Abinda Obasanjo ya yi ya dace. Dalili shi ne, duk abin da ka yi ra’ayi kamata ya yi ka fito fili ka nuna wa duniya don wasu su yi koyi da kai. Ka ga daga lokacin da Obsanjo ya yaga katin jam’iyyar PDP, wani mutum daga Jihar Gombe ya yi koyi da shi, shi ma ya fito ya yaga katinsa na PDP. Wannan shi ne abin da ya kamata a yi wa jam’iyyar PDP.”