Yaga katin PDP na Obasanjo ya haifar da rudani a Jihar Jigawa
Yaga katin zama dan Jam’iyyar PDP da tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi ya haifar da rudani tsakanin magoya bayan jam’iyyar a Jihar Jigawa, lamarin da ya sa Gwamnan Jihar Alhaji Sule Lamido kiran taron gaggawa a gidan gwamnati tare da duk masu fada-a-ji na jam’iyyar. Taron wanda aka shafe tsawon awa biyar ana […]
Yaga katin zama dan Jam’iyyar PDP da tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi ya haifar da rudani tsakanin magoya bayan jam’iyyar a Jihar Jigawa, lamarin da ya sa Gwamnan Jihar Alhaji Sule Lamido kiran taron gaggawa a gidan gwamnati tare da duk masu fada-a-ji na jam’iyyar.
Taron wanda aka shafe tsawon awa biyar ana yi, babu wanda ya fada wa manema labarai inda aka kwana, kuma wakilimmu ya ga ’ya’yan jam’iyyun adawa suna shiga da fita daga gidan gwamnatin jihar
Wakilinnamu ya tuntubi kakakin Gwamnan Jihar Malam Umar Kiyari Jitau Madamuwa kan abin da aka tattauna a wurin taron, inda ya ce ba ya da labarin komai, kuma Gwamna ne ya kamata ya amsa ta, kuma akwai yiwuwar zai yi wa manema labarai bayani.
dan takarar Gwamnan Jihar karkashin Jam’iyyar GDM Alhaji Sardauna Yaro ’Yanleman ya ce jam’iyyun adawa ciki har da APC da jam’iyyuarsu sun fara zawarcin Obasanjo, bayan da ya share wa magoya bayansa hanyar ficewa daga PDP, wadda ga alama karshenta ya zo.