Yagya Bahadur: Mutumin da ke iya lasar goshinsa da harcensa

Wani mutum da aka bayyana ya fi kowa tsawon harce a duniya mai suna Yagya Bahadur Katuwal, mai shekara 35 yana tattare da abin al’ajabi kan yadda yake sarrafa harscensa. A yayin da wadansu ke nuna bajintarsu ta amfani da harcensu, su lashi hancinsu, shi kuwa wannan mutumin fasaharsa ta wuce tasu, inda ya fito […]

Yagya Bahadur: Mutumin da ke iya lasar goshinsa da harcensa

Wani mutum da aka bayyana ya fi kowa tsawon harce a duniya mai suna Yagya Bahadur Katuwal, mai shekara 35 yana tattare da abin al’ajabi kan yadda yake sarrafa harscensa.

A yayin da wadansu ke nuna bajintarsu ta amfani da harcensu, su lashi hancinsu, shi kuwa wannan mutumin fasaharsa ta wuce tasu, inda ya fito da sabon salo na lasar goshinsa da harcensa saboda tsawon harcen da yake da shi.

Yagya Bahadur Katuwal da ke zaune a birnin Urlabari na Lardin Morang a kasar Nepal yana amfani da harcensa ya lashi goshinsa.

Katuwal mai sana’ar tukin motar bas a garin Urlabari a kasar Nepal, sai dai ba ya lasar goshinsa da harcen a ko’ina saboda hakan yana firgita kananan yara.

Yagya Katuwal dai tun lokacin da ya fara tukin bas ta wata makaranta, sai harcensa ya zama wani abin al’ajabi ta yadda yake amfani da shi yadda yake so. Wannan ya sa wadansu abokansa suka fara saka bidiyon yadda yake yi da harcen a shafukan sadarwa na zamani.

An tabbatar da cewa, Yagya shi ya fi kowa tsawon harce kuma shi kadai ne a duniya yake iya amfani da harcensa ya lashi goshinsa.

Sai dai a wurin aikinsa an gargade shi da kada ya nuna baiwar da Allah Ya yi masa saboda gudun firgita daliban makarantar.

A duk lokacin da Yagya yake nuna bajintarsa idan yara suka gan shi wani lokaci har fitsari suke yi.

Yagya ya ce, “Ina alfahari da baiwar da Allah Ya ba ni, zan iya rufe hancina da lebena tare da lasan goshi na da harcena, yayin hakan zan iya fitar da wani sauti daban lokacin da na zaro harcen waje.”

Yagya ya kara da cewa, “Idan har zan iya fitowa a shirin fim din al’ajabi ba na bukatar in yi shiga ta ban-tsoro kamar yadda wadansu ’yan wasa ke yi.” A koyaushe bai yarda cewa, ra’ayoyin wadansu ya shafe shi ba saboda ya  yarda da baiwar da yake da ita.

Yagya ya ce, nan gaba yana sa ran samun karramawar da ake bai wa wadanda suka shahara a duniya  ta shiga Kundin Abubuwan Ban Mamaki na Duniya (Guinness World of Record).

Hamas da Isra’ila sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

HOTUNA: Yadda aka yi bikin tunawa da mazan jiya a faɗin Nijeriya

Sanusi zama daram kuma Sarki ɗaya tilo a Kano — Falana

An rantsar da Shugaban Mozambique Daniel Chapo