Yahaya Bello ba ya hannunmu, nemansa muke ruwa a jallo — EFCC

Hukumar ta ce har yanzu neman tsohon gwamnan ta ke ruwa a jallo.

Yahaya Bello ba ya hannunmu, nemansa muke ruwa a jallo — EFCC

Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), ta ƙaryata iƙirarin da tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ya yi na cewar ya amsa goron gayyatar da ta aike masa.

Hukumar ta bayyana cewa har yanzu tana neman tsohon gwamnan bisa zargin karkatar da Naira biliyan 80.2.

Kakakin hukumar, Dele Oyewale ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya aike wa ’yan jarida a ranar Laraba.

Tun da farko, ofishin yaɗa labaran Bello, ya fitar da wata sanarwa da safiyar ranar Laraba, inda ya ce tsohon gwamnan ya yanke shawarar amsa gayyatar EFCC bayan tattaunawa da iyalansa da lauyoyinsa.

Ofishin ya kuma yi alƙawarin yin cikakken bayani game da ganawar Bello da EFCC nan gaba.

Sanarwar, wanda Daraktan Ofishin Yaɗa Labaran Yahaya Bello, Ohiare Michae, ya sanya wa hannu, ta kuma buƙaci EFCC ta kasance mai ƙwarewa da mutunta haƙƙin tsohon gwamnan a matsayinsa na ɗan ƙasa.

Amma da yake mayar da martani kan iƙirarin, kakakin hukumar ya ce babu yadda za a aike wa mutumin da ake nema ruwa a jallo, goron gayyata.

Oyewale ya ce, “Rahotannin da ke yawo cewar Yahaya Bello yana hannun EFCC ba gaskiya ba ne.

“Hukumar tana son bayyana cewa Bello ba ya hannunta. Ana ci gaba da neman shi kan zargin karkatar da Naira biliyan 80.2, tare da sammacin kama shi.”

Kashim Shettima zai jagoranci tawagar Nijeriya a taron MDD

NECO ta fitar da sakamakon jarrabawar 2024

Kano: Abba ya rusa ciyamomin riko

An haramta wa ma’aikatan Asibitin Tarayya yin ‘kirifto’ a wurin aiki