Yahaya Bello: Babu kuɗin da ya bace a asusun Kogi —Majalisa ga EFCC

Majalisar Dokokin Jihar Kogi ta ƙaryata zargin wawushe kuɗi da EFCC ke wa tsohon Gwamna Yahaya Bello, inda ta ce babu kudin da ya bata daga asusun jihar

Yahaya Bello: Babu kuɗin da ya bace a asusun Kogi —Majalisa ga EFCC

Majalisar Dokokin Jihar Kogi ta ƙaryata zargin wawushe kuɗi da ake yi wa tsohon Gwamna Yahaya Bello, inda ta bayyana cewa babu kudin da ya bata daga asusun jihar.

“Babu wani kudi da ya bace daga asusun Kogi da zai sa a gurfanar da shi a gaban kotu,” a cewar ’yan majalisar a zamansu na ranar Litinin.

Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙin Kasa Zagon Ƙasa (EFCC) ta yi ƙarar Yahaya Bello a gaban Babban Kotun Tarayya da ke Abuja, bisa tuhume-tuhume 19 na halasta kudaden haram.

’Yan majalisar sun yi kira da a yi taka-tsan-tsan wajen gurfanar da tsohon gwamnan a gaban kuliya.

Mambobin majalisar guda biyu, Akus Lawal da Jacob Olawunmi, a wani kuduri, sun bayyana damuwa game da shari’ar ta Yahaya Bello.

Lawal ya kara da cewa EFCC na son “kaskantar da Gwamna Usman Ododo da tsohon Gwamna Yahaya Bello”.

Olawumi ya jaddada cewa gwamnatin jihar ta wallafa rahoton kudin jihar da aka tantance, kuma “Majalisar dokokin Kogi za ta iya cewa babu wani kudi da ya bata,” in ji shi.

Sauran ’yan majalisar da suka yi magana kan batun, sun ce EFCC na da “wata manufa ta daban, lura da yadda take tafiyar da batun shari’ar Bello.”

Honorabul Yahaya Umar, a nasa gudunmuwar, ya ce hukumar ta dauki matakin ne domin zuabr da kimar jihar Kogi.

“Abubuwan da suka faru a lokacin da aka kama Bello ya nuna cewa ana kai masa hari,” in ji shi.

Mataimakiyar shugaban majalisar, Comfort Nwuchiola Egwaba, ta yi zargin cewa ana nemabn bata sunan Yahaya Bello ta kafofin yada labarai, saboda “EFCC na da ajanda da take bi.”

Majalisar ta fusata kan yunkurin EFCC na cafke Yahaya Bello a ranar 17 ga Afrilu da 18 ga Satumba.

Ta yi Allah-wadai da harin da aka kai gidan gwamnan jihar a Abuja, inda ta bukaci hukumar EFCC da ta rika kiyaye doka da oda.

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja