Yahudawan waje da masu kamun kafa ke jawo rikicin Gabas ta Tsakiya – Yarima Charles
Yariman mai jiran gado na Birtaniya, Yarima Charles ya zargi “Yahudawan waje” da haddasa rikicin Gabas ta Tsakiya inda ya yi kira ga Amurka ta “dauki mataki a kan Yahudawa ’yan kamun kafa.” Wata wasika da Yarima Charles ya rubuta a 1986 wadda aka buga ta a karon farko a jaridar Mail on Sunday ta […]
Yariman mai jiran gado na Birtaniya, Yarima Charles ya zargi “Yahudawan waje” da haddasa rikicin Gabas ta Tsakiya inda ya yi kira ga Amurka ta “dauki mataki a kan Yahudawa ’yan kamun kafa.”
Wata wasika da Yarima Charles ya rubuta a 1986 wadda aka buga ta a karon farko a jaridar Mail on Sunday ta Birtaniya a ranar Lahadin da ta gabata an rubuta ta ce, ga wani babban aminin Yarima kuma mashawarcinsa Sa Laurens Jan ban der Post, kuma ta kunshi bayan da ba saba gani ba a baya game da ra’ayin Yariman kan rikicin da ke tsakanin Larabawa da Yahudawa a Gabas ta Tsakiya kamar yadda jaridar Newsweek ta ruwaito a ranar Lititin da ta gabata.
“A yanzu na fahimci cewa Larabawa da Yahudawa ’yan uwan juna ne tun asali, kuma kwararar baki, Yahudawan Yammacin Turai (musamman daga Poland kamar yadda suka ce) ta taimaka wajen jawo babbar matsala,” Yariman ya rubuta a wasikar bayan ya dawo daga ziyarar da ya kai Saudiyya da Bahrain da katar.
Yariman ya bayyana ziyarar da “abar burgewa” ya ce, ya karu da abubuwa da dama game da Gabas ta Tsakiya da kuma al’ummar Larabawa, kuma ya yi kokarin karanta Alkur’ani. Kuma ya bayyana cewa zai yi wuya a kawar da ta’addanci matukar ba a magance abin da yake jawo shi ba.
“Shin ko zai yiwu wadansu shugabannin Amurka su tashi tsaye su dauki mataki a kan Yahudawa ’yan kamun kasa a Amurka?” Yariman ya yi tambaya a wasikar.
Sai dai Yahudawa masu sharhi sun mayar da martani cikin gaggawa ga Yariman, inda suka bayyana wasikar tasa da ta nuna kiyayya ga Yahudawa, musamman amfani da kalmar ‘Yahudawa ’yan kamun kafa,’ inda ya nuna Yahudawan suna tsoma baki sosai a harkokin da suke faruwa a sassan duniya.
“A wurina kalmar ‘Yahudawa ’yan kamun kafa’ daya ce daga cikin kalmomin nuna kiyayya ga Yahudawa da ake amfani da ita a karnoni da dama. Wannan ce tatsunniya da ake yayatawa cewa akwai manyan Yahudawa da suke juya harkokin kasashen waje ko kafafen watsa labarai ko bankuna ko kowane abu,” Stephen Pollard, editan jaridar Yahudawa ta The Jewish Chronicle, ya rubuta don mayar da martini kan wasikar Yariman.