Yajin Aiki: Ƙungiyar Ƙwadago Za Ta Bi Sahun SSANU Da NASU
Gwamnatin Tarayya ta gaza cika yarjejeniyar da suka kulla da ita tun a shekarar 2009.
Ƙungiyar Ƙwadago (NLC) ta yi barazanar bin sahun ma’aikatan jami’a na (SSANU) da (NASU) da suka tsunduma yajin aikin gargaɗi.
Aminiya ta rawaito cewa, a jiya Litinin ce kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’a (SSANU) da ta Ma’aikatan da ba Malamai ba (NASU) suka soma yajin aiki sanadiyar wofantar da yarjejeniyarsu da Gwamnatin Tarayya ta yi wadda aka kulla tun a shekarar 2009.
Da yake karin haske kan lamarin, Shugaban Kungiyar Kwadagon, Joe Ajaero, ya ce nuna wariya da gwamnatin ta yi wajen biyan wata kungiyar ta bar wata abu ne da ko kadan bai dace ba.
Kwamared Ajaero ya kuma bayyana takaici kan yadda gwamnatin tarayya take barin iyaye da daliban jami’o’in cikin matsala idan irin haka ta faru, alhali kuskuren nata ne.
“Mun lashi takobin bin sahun takwarorinmu (NASU) da (SSANU) domin tabbatar da an biya su albashinsu da aka rike musu ba tare da wani tartibin bayani kan hakan ba.
“Muna sane da halin da ’ya’yan kungiyar suka shiga da iyalinsu sakamakon hakan a baya.
“Wani abun takaicin shi ne yadda gwamnatin ta ware wasu ta biya su wasu kuma ko oho, domin kawo musu rarrabuwar kai babu gaira ba dalili.
“A yanzu da ake yi wa wannan gwamnatin kyakkyawan zato, kamata ya yi ta tabbatar da ba a shiga wani yajin aikin ba. Don haka muke kira gare ta da ta biya su basussukan da suke bi ba tare da bata lokaci ba,” a cewar Ajaero.