Yajin Aiki: ASUU ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwana 14

Ƙungiyar ta ce tana fatan gwamnati ta magance matsalolin da suke fuskanta.

Yajin Aiki: ASUU ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwana 14

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwana 14 don warware matsalolin da ke ci gaba da addabar malaman jami’o’i.

Wannan ya biyo bayan ƙarewar wa’adin kwana 21 da ƙungiyar ta bai wa gwamnatin a baya.

Ƙungiyar na neman a kammala tattaunawa kan yarjejeniyar 2009 tsakanin Gwamnatin Tarayya da ASUU, bisa ga sabuwar yarjejeniyar kwamitin Nimi Briggs na 2021.

Kazalika, suna buƙatar a biya su albashin da aka riƙe saboda yajin aikin da suka yi na tsawon watanni takwas a 2022.

Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, ya bayyana takaicinsa kan rashin jajircewar gwamnati kan warware matsalolinsu.

A cewarsa, “Saboda haka, ASUU ta yanke shawarar sake bai wa Gwamnatin Tarayya wani wa’adin kwanaki 14, a kan ƙarin kwanaki 21 da aka bayar a baya, wanda zai fara daga ranar Litinin, 23 ga watan Satumba, 2024.

“Ƙungiyar ba za ta ɗauki alhakin duk wani rikici da zai taso ba idan har gwamnati ta kasa yin amfani da wannan dama da ASUU ta ba ta don daƙile rikicin da ke ƙoƙarin tasowa.”

ASUU na kuma neman a biya malaman da ke aikin wucin gadi, da kuma yi wa sabbin waɗanda aka ɗauka aiki ƙarin albashin da aka riƙe musu saboda tsarin biyan albashin gwamnati (IPPIS).

Haka kuma, suna buƙatar a biya bashin da suke bi na kuɗin haɗin gwiwa da sauran hakkoki.

Sauran buƙatun sun haɗa da samar da kuɗaɗe don farfado da jami’o’in gwamnati, biyan alawus ɗin da aka musu alƙawari a kasafin kuɗin 2023, dakatar da gina jami’o’i ba bisa ƙa’ida ba.

Ƙungiyar tana kuma so a maye gurbin tsarin IPPIS da tsarin UTAS.

Sojin sama sun yi kuskuren kashe mutum 16 a Zamfara

Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7