Yajin aiki: kungiyar dalibai na barazanar kin zaben Buhari a 2019

Kungiyar daliban jami’o’in Najeriya NANS na yin barazanar kin zaben Shugaba Buhari a zaben 2019  idan har bai biya bukatun kungiyar malaman jami’o’in Najeriya ASUU da kungiyar malaman kwalejojin ilimi ba. Kakakin kungiyar daliban Azeez Adeyemi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a garin Abeokuta babban birnin jihar Ogun, bayan wani gangami da kungiyar […]

Yajin aiki: kungiyar dalibai na barazanar kin zaben Buhari a 2019

Kungiyar daliban jami’o’in Najeriya NANS na yin barazanar kin zaben Shugaba Buhari a zaben 2019  idan har bai biya bukatun kungiyar malaman jami’o’in Najeriya ASUU da kungiyar malaman kwalejojin ilimi ba.

Kakakin kungiyar daliban Azeez Adeyemi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a garin Abeokuta babban birnin jihar Ogun, bayan wani gangami da kungiyar ta yi akan rashin biyan bukatun Kungiyar ASUU da Gwamnatin tarayya ta yi.