Yajin Aiki: Shugaban ’Yan Sanda ya gargaɗi NLC da TUC
Ƙungiyoyin ƙwadagon sun tsunduma yajin aikin a ranar Litinin.
Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya gargaɗi ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC kan yajin aikin da suka shiga a ranar Litinin.
Egbetokun, ya ce matakin da ƙungiyoyin suka ɗauka na iya haifar da tashe-tashen hankula da rashin zaman lafiya, wanda hakan ka iya haifar da karya doka da oda a ƙasar nan.
- Yajin Aiki: Gwamnatin Tarayya da NLC na ganawar sirri
- NLC na neman durƙusar da arziƙin Najeriya — Fadar Shugaban Ƙasa
Egbetokun, wanda ya yi magana ta bakin mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi, ya ce ya kamata shugabancin ƙungiyar ƙwadago su koma teburin sulhu da gwamnati domin samun matsaya.
Ya ce, “Bisa la’akari da sanarwar da gwamnatin tarayya ta fitar cewa yajin aikin an shige sa ba bisa ƙa’ida ba, rundunar ‘yan sandan Najeriya na kallon wannan matakin a matsayin wani abu da zai iya haifar da tashin hankali da rashin zaman lafiya.
“Hukumar ‘yan sanda ta buƙaci ƙungiyar ƙwadago da ta ci gaba da tattaunawar da ake yi da ita, kan sabon mafi ƙarancin albashi ma’aikata, da kuma janye yajin aikin da ta fara don gujewa sake dagula matsalolin matsin rayuwa da ake fama da su.”
Da yammacin ranar Litinin, Gwamnatin Tarayya ta yi wata ganawa da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC a Abuja, kan yajin aikin da suka tsunduma.
Ganawar wadda ke gudana a yanzu, ta haɗa da shugaban NLC, Joe Ajaero da takwaransa na TUC, Festus Osifo.
A ɓangaren gwamnati akwai sakataren gwamnatin tarayya, George Akume; ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris Malagi; ministan ƙwadago, Nkiruka Onyejeocha; da sauransu.
Al’amuran yau da kullum da suka shafi harka filin jirgin sama, jami’o’i, asibitoci da wutar lantarki sun durƙushe bayan da ƙungiyoyin suka shiga yajin aikin a ranar Litinin.
Idan ba a manta ba, Gwamnatin Tarayya, ta amince da Naira 60,000 a matsayin mafi ƙarancin albashin, sai dai NLC ta yi fatali da wannan buƙatar.
NLC ta fusata ne bayan ƙoƙarin tatatunawa da Gwamnatin Tarayya domin cimma yarjejeniya dangane da mafi ƙarancin albashin ya gagara, ganin yadda gwamnatin ta dage kan cewar Naira 60,000 kawai za ta iya biya.
Amma a wani martani da Gwamnatin Tarayya ta yi ta hannun mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, ya ce buƙatar ta NLC da TUC ba za ta yi komai ba face kassara tattalin arziƙin ƙasar nan.
Ngelale, ya ce matuƙar gwamnati za ta biyewa buƙatar ƙungiyoyin ƙwadagon, tabbas wasu daga cikin kamfanoni masu zaman kansu za su rufe, abin da zai zamarwa ƙasar nan matsala a maimakon samun ci gaba.
Ya ce ko a yanzu Najeriya na fama da tsadar kayan abinci da sauran kayan buƙata, kuma babu makawa wannan lamarin zai ƙaru matuƙar aka yi ƙarin albashin da ƙungiyar ƙwadago ke buƙata.