Yajin aiki ya janyo tsaiko a shari’ar A’isha dankano da darakta Mu’azzam

Shari’ar da ake yi tsakanin jaruma A’isha dankano da darakta Mu’azzam Idi Yari a Babbar Kotun Majistare da ke unguwar Nomansland a birnin Kano ta samu tsaiko sakamakon yajin aikin da ma’aikatan kotu suka fara tun a ranar 2 ga Janairu, 2015. A zaman karshe na kotun an sanya ranar 14 ga Fabrairu, 2015 a […]

Yajin aiki ya janyo tsaiko a shari’ar A’isha dankano da darakta Mu’azzam
Yajin aiki ya janyo tsaiko a shari’ar A’isha dankano da darakta Mu’azzam

Shari’ar da ake yi tsakanin jaruma A’isha dankano da darakta Mu’azzam Idi Yari a Babbar Kotun Majistare da ke unguwar Nomansland a birnin Kano ta samu tsaiko sakamakon yajin aikin da ma’aikatan kotu suka fara tun a ranar 2 ga Janairu, 2015.

A zaman karshe na kotun an sanya ranar 14 ga Fabrairu, 2015 a matsayin ranar da za a ci gaba da shari’ar, amma sakamakon yajin aiki da bangaren shari’a ke yi ya sanya ba a yi zaman kotun ba.
A yanzu dai za a ci gaba da jira har zuwa lokacin da ma’aikatan kotu za su janye yajin da aikin da suke yi.
Idan ba a manta ba dai darakta Mu’azzam Idi Yari ya shigar da kara gaban kotun ne bisa zargin jaruma A’isha dan Kano ta bata masa suna a wajen daukar wani fim a ranar 23 ga watan Satumba, 2014.
A zaman farko na kotun wanda aka yi shi a ranar 29 ga watan Satumba, 2014 an tuhumi jarumar da yi wa daraktan yarfen cewa yana watsewa da ’yan fim mata masu yawa, sannan ba don sana’ar fim da yake yi ba, to da haka zai kare rayuwarsa a matsayin mabaraci a bakin kasuwar ’yan kura. Laifukan da ake zargin jarumar sun saba sashe na 392 da sashe na 399 na cikin kundin tsarin mulki na final kod.
A lokacin zaman kotun jarumar ta musanta laifukan da ake zargin ta da aikatawa, inda alkalin kotun Muktar dandago ya bayar da belinta a kan sharadin sanya hannu da ta yi cewa za ta yi zaman lafiya tsakaninta da mai karar har na tsawon shekara biyu.
Sai dai a zaman kotun na biyu mai karar ya shaida wa kotu cewa jarumar ta shiga har dakinsa a otel a yayin da suka ziyarci Jamhuriyyar Nijar a lokacin bikin sallar bara, inda ta rika zazzaga masa ashariya.
Ya kuma shaida wa kotu cewa ya dauki muryar jarumar da wayarsa a lokacin da take zagin sa, inda ya nemi kotu ta amince masa ya bayyana shaidarsa, lamarin da alkali ya amince. A nan take kowa da yake kotun ya ji irin zagin da wacce ake zargi ta yi wa mai kara.
Alkalin ya janye batun belin da kotun ta bayar ga jarumar tun farko, saboda samun ta da keta alfarmar alkawarin da ta dauka tun farko, don haka ya bayar da umarnin sakaya ta a kurkuku. Sannan ya dage sauraren shari’ar zuwa ranar 4 ga watan Nuwamba, 2014.
Daga baya an bada belin jarumar hade da ci gaba da sauraren shari’ar.
A zaman kotun na karshe kafin a sake dagewa, daraktan ya gabatar da shaidarsa ta farko wato jaruma A’isha Aliyu Tsamiya, sannan aka nemi ya gabatar da shaidarsa ta biyu.
Yanzu dai abin jira a gani shi ne lokacin da ma’aikatan kotu za su janye yajin aikinsu.

A-Kurkura: Guba ko Magani?

Tsohon Shugaban Jami’ar Ilori, Farfesa Ambali ya rasu

ICPC ta hana El-Rufai ganin likita —Hadiminsa

Hanyoyin zuwa Katsina sun zama tarkon mutuwa