Yajin aiki: Maniyyatan Najeriya na cikin rashin tabbas

Ma’aikatan sufurin jiragen sama sun shiga yajin aiki mako guda kafin a kammala kwashe maniyyatan Najeriya zuwa Saudiyya

Yajin aiki: Maniyyatan Najeriya na cikin rashin tabbas

Jigilar maniyyatan Najeriya zuwa Saudiyya ta shiga rudani bayan kungiyoyin kwadagon kasar sun tsunduma yajin aiki a safiyar Litinin.

Ma’aikatan sufurin jiragen sama sun Fara yajin aikin ne a yayin da ya rage mako guda a kammala da jigilar maniyyatan Najeriya zuwa Kasa Mai Tsarki.

Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta bayyana 10bga watan Yuni 2024 a matsayin ranar da za ta kammala jigilar maniyyatan kasar domin sauke farali.

Tun a daren Lahadi kungiyoyin ma’aikatan sufurin jiragen sama suka umarci mambobinsu su dakatar da aiki daga karfe 12 na dare a fadin Najeriya.

Kungiyoyin manya da kananan ma’aikata, injiniyoyi, matuka jirage da ma’aikatan jigila da sauransu sun ba da umarnin ne bayan wani taron gaggawa da suka gudanar.

Sanarwar hadin gwiwar da suka fitar dauke da sa hannun Kwamared Ocheme Aba, (NUATE);  Frances Akinjole, (ATSSSAN); Abdul Rasaq Saidu, (ANAP) da kuma Olayinka Abioye (NAAPE) ta umarci daukan rassan kungiyoyin su bi umarninn fara yajin aikin 100%.

Hakan na zuwa ne duk da cewa sanya bakin da jagororin majalisar dokoki ta kasa domin janye yakin aikin bai yi nasara ba.

Majalisar ta kira zaman ne domin lallashin shugabannin kungiyar kwadago na NLC da TUC su amince da tattaunawa da bangaren gwamnati kan dambarwar mafi karancin albashi.

Ministoci da manyan jami’an gwamnati daga fadar shugaban kasa sun halarci zaman wanda a karshe aka tashi ba tare da an cimma matsaya ba.

A yayin zaman shugabannin kwadago sun shaida wa taron cewa za a ci gaba da yajin aikin sannan a ci gaba da tattaunawa kan lamarin.

Ana iya tuna cewa kungiyoyin kwadagon sun ba wa gwamnatin wa’adin ranar 29 ga watan Mayu ta aiwatar da sabon mafi karancin albashi na Naira 620,000.

Kungiyoyin sun sanya sabon mafi karancin albashin ne bisa la’akari da janye tallafin mai na da wutar lantarki da gwamnati ta yi, da kuma faruwar darajar Naira da tashin Dala da suka haifar da ninkuwar farashin kayayyaki da matsanancin tsadar rayuwa a kasar.

Da farko gwamnatin ta yi wa ’yan kwadagon tayin mafi karancin albashin Naira 48,000 kafin daga bisani ta kara zuwa Naira 56,000.

Kungiyar kwadagon ta bayyana tayin Gwamantin a matsayin rainin wayo tana mai cewa abin da ta gabatar shi ne mafi karancin abin da zai iya daukar dawainiyar karamin ma’aikaci da iyalansa mutum biyar.

Sojin sama sun yi kuskuren kashe mutum 16 a Zamfara

Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7