Yajin aiki: Yau za a tattauna da kungiyar ASUU da Gwamnati
Kungiyar malaman jami’o’in Najeriya ASUU yau zata ci gaba da tattaunawa da Gwamnatin tarayya don bin hanyoyin dakatar yajin aikin da malaman jami’o’in suke yi. Shugaban kungiyar ASUU Farfessa Biodun Ogunyemi ya sanarwa majiyarmu cewa, an shirya tattaunawar ne da misalin karfe 1 na rana tare da Ministan ilimi Malam Adamu Adamu da kuma sauran […]
Kungiyar malaman jami’o’in Najeriya ASUU yau zata ci gaba da tattaunawa da Gwamnatin tarayya don bin hanyoyin dakatar yajin aikin da malaman jami’o’in suke yi.
Shugaban kungiyar ASUU Farfessa Biodun Ogunyemi ya sanarwa majiyarmu cewa, an shirya tattaunawar ne da misalin karfe 1 na rana tare da Ministan ilimi Malam Adamu Adamu da kuma sauran mukarraban Gwamnati.