Yajin aikin ASUU: Dalibai sun fantsama zanga-zanga a titunan Legas
Sun kuma yi barazanar mamaye tituna in ba a sasanta ba
Daliban Jami’ar Legas (UNILAG) sun fantsama tituna suna zanga-zanga tare da yin kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kawo kawo karshen yajin aikin Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU).
Matakin dai ya biyo bayan ASUU ta sanar da kara tsawaita yajin aikin nata da wata uku ranar Litinin, inda daliban suka fito kan tituna suna wake-waken neman a sasanta don su koma makaranta.
- ASUU ta sake tsawaita yajin aikinta har zuwa watan Agusta
- ASUU ta yi barazanar daina yi wa INEC aikin zabe
Wasu daga cikin masu zanga-zangar dai na rike da kwalaye masu dauke da rubuce-rubuce kamar ‘Yajin aiki ya lalata bangaren ilimi, muna bukatar komawa makaranta, ‘Mun gaji da gwamnati da ASUU’ da dai sauransu.
Hakazalika sun yi barazanar tare tituna muddin gwamnati ba ta saurare su ba.
Ga wasu daga cikin hotunan: