Yajin aikin Gidajen Burodi bai dace ba – Shugaban Masu Shayi
Shugaban kungiyar Masu Shayi ta kasar nan Alhaji Shu’aibu Abubakar ya bayyana cewa tafiya yajin aikin da kungiyar Masu Gidajen Burodi ta yi a wasu jihohin kasar nan, ba su yiwa wa talakawan Najeriya adalci ba. Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu. Ya ce “domin talakawa ne suke cin […]
Shugaban kungiyar Masu Shayi ta kasar nan Alhaji Shu’aibu Abubakar ya bayyana cewa tafiya yajin aikin da kungiyar Masu Gidajen Burodi ta yi a wasu jihohin kasar nan, ba su yiwa wa talakawan Najeriya adalci ba.
Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu. Ya ce “domin talakawa ne suke cin burodin da suke yi, don haka bai kamata a ce sun tafi yajin aiki ba a yanzu.”
Daga nan ya ce ba wannan sabuwar gwamnati ce ta haddasa wannan al’amari na tashin farashin kayayyakin yin burodin ba. Kuma ba yau aka fara samun hauhawar kayayyakin ba. Ya ce “Ko a lokacin gwamnatin da ta gabata sai da buhun sukari ya taba kai naira dubu 10, fulawa kuma ta taba kai har naira dubu tara, amma ba su tafi yajin aiki ba, sai a wannan karo. Ba kayayyakin yin biredi ne kawai suka samu karin farashi ba, kayayyaki da dama sun tashi. Kamar mu masu shayi mun fi su amfani da kayayyaki da yawa. Misali muna amfani da madara da ganyen shayi da banbita da milo da dai sauransu kuma duk farashinsu ya tashi. Amma mu ba mu yi kuka ba, sai su da suka sami karin farashin fulawa da sukari kawai,” inji shi.
Alhaji Shu’aibu ya ce kamata ya yi su tuntube su a matsayinsu na masu hulda da su kafin su dauki wannan mataki, amma sai ya ce ba su yi hakan ba.