Yajin aikin kungiyar malaman jami”o”i (ASUU) ya tsayar da komai a jami”o”i
Kungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU ta fara yajin aiki inda hakan ya kawo cikas ga jarabawar da wasu jami’o’in suke yi. Malaman sun zargi Gwamnatin Tarayya da gaza cika yarjejeniyar da ta yi da kungiyar tun shekarar 2009. Kungiyar ta dauki matakin shiga yajin aikin a taron gaggawa da shugabannin kungiyar na kasa suka gudanar […]
Kungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU ta fara yajin aiki inda hakan ya kawo cikas ga jarabawar da wasu jami’o’in suke yi.
Malaman sun zargi Gwamnatin Tarayya da gaza cika yarjejeniyar da ta yi da kungiyar tun shekarar 2009.
Kungiyar ta dauki matakin shiga yajin aikin a taron gaggawa da shugabannin kungiyar na kasa suka gudanar jiya a Abuja.
Shugaban Kungiyar Malaman Jami’o’in ta ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi ya bayyana wa manema labarai jiya cewa yajin aikin ya fara nan take kuma yajin aiki ne na bai-daya.
“Babu koyarwa, ba jarabawa kuma ba gudanar da wani taro har sai gwamnati ta biya bukatun kungiyarmu”. Inji shi
Da take yi wa Aminiya karin bayani, Daraktan Yada Labari ta Ma’aikatar Ilimi, Misis Chinenye Ihuoma ta ce kwamitin mutum 16 da gwamnati ta kafa kan lamarin yana ci gaba da gudanar da aiki tare da kungiyar.
Shi ma Shugabanm Kwamitin da Gwamnatin Tarayyar Ta kafa don sasanta yarjejeniyar shekarar 2009 da kungiyar, Babban Lauya Wale Babalakin ya bayyana cewa shiga yajin aikin da kungiyar ta yi mayar- da- hannun-agogo-baya ne.
Yajin aikin ya yi tasiri kwarai da gaske a jami’ar Bayero da ke Kano da ta Ahmadu Bello da ke Zariya da ta Jami’ar Ibadan da ke jihar Oyo da sauran jami’o’i da ke sassan kasar nan.