Yajin aikin ma’aikatan mai ya rage hako shi da rabi a Libya – Minista
Ministan Mai na kasar Libya Abdelbari Al Arusi ya ce yajin aiki da ma’aikatan mai ke yi a gabashin kasar ya jawo raguwar hakar mai da rabin abinda ake haka.Al Arusi ya bayyana haka ne a tattaunawa da wani gidan talabijin, inda ya ce hakar mai ta yi kasa da ganga dubu 665 a kullum […]
Ministan Mai na kasar Libya Abdelbari Al Arusi ya ce yajin aiki da ma’aikatan mai ke yi a gabashin kasar ya jawo raguwar hakar mai da rabin abinda ake haka.
Al Arusi ya bayyana haka ne a tattaunawa da wani gidan talabijin, inda ya ce hakar mai ta yi kasa da ganga dubu 665 a kullum sakamakon yajin wata daya da masu gadi da ke dauke da makamai suke yi wadda ta jawo rufe tashoshin jigilar mai da suke jigilar ganga miliyan daya da dubu 550 kafin yakin basasar Libya na shekarar 2011 kamar yadda ya shaida wa gidan talabijin na Al Hurra.
Al Arusi ya ce kafin zanga-zangar, Libya ta inganta hakar mai, kuma tsadar mai ta sanya Libya ta samu karin Dala biliyan uku kan kudin shigar da ta sa ran samu a wata shida na farkon bana.
Arusi ya ce idan yajin aikin ya yi tsawo zai iya jawo tasgaro ga kasafin kudin kasar. Kuma ya zargi ma’aikatan da ba na mai ba da masu akidar federaliyya a kasar da jawo yajin aikin ma’aikatab man wanda ya ce ya jawo asarar kudin shiga ga kasar ta kimanin Dala biliyan biyu (kimanin Naira biliyan 320).
“Wadannan kungiyoyi sun bayyana tsarin federaliyya ba su amince da gwamnatin tsakiya ko majalisar kasa ba. Wadannan matasa sun mallaki makamai suna da sojoji, kuma da karfi suka hana mu fitar da mai suka rufe tashoshin dakon mai,” inji shi.
Ya ce masu zanga-zangar sun tuntubi tankokin dakon mai kan su dauki man bisa zargin cewa jami’an gwamnatin kasar suna karkatar da kudin man zuwa asusun ajiyarsu, amma kamfanonin mai na kasa da kasa sun ki amincewa da wannan tayi.
Ya ce tuni Firayi Ministan kasar Ali Zeidan ya kafa kwamitin bincike don bin bahasin wannan korafi nasu.
Ministan ya ce, tashoshin dakon mai da suka hada da Es Sider da Ras Lanuf da Zueitina da kuma Marsa Al Hariga da suke gabashin kasar inda mafi yawan man yake suna rufe, inda ta Marsa Al Brega ce kawai ke bude, yayin da rijiyoyin main a Zawiya da Mellitah da ke Kudancin kasar suke aiki.