Yajin aikin malaman jami’a: Su janye ko su canja salo?
An dauki lokaci mai tsawo da malaman jami’a ke cikin yajin aiki. Duk da cewa suna ta tattaunawa tsakaninsu da gwamnati amma abin ya ci tura, suna ci gaba da yajin aiki, dalibai na zaune dirshan a gidajensu. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace malaman su janye daga yajin aikin ko kuwa […]
An dauki lokaci mai tsawo da malaman jami’a ke cikin yajin aiki. Duk da cewa suna ta tattaunawa tsakaninsu da gwamnati amma abin ya ci tura, suna ci gaba da yajin aiki, dalibai na zaune dirshan a gidajensu. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace malaman su janye daga yajin aikin ko kuwa su canja salo? Wakilanmu sun tattauna da al’umma kan haka kuma ga ra’ayoyinsu kamar haka:
Kada ASUU su sassauta – Nasir G. Ahmad
Nasir G. Ahmad: “Duk sa’ad da aka kai wasu ma’aikatan gwamnati bango har suka shiga yajin aiki, ba a duba laifin gwamnati, a yi kira gare ta da ta biya musu bukatunsu, wanda amfaninsu zai dawo ga daukacin al’umma, sai a dora laifin baki daya kan ma’aikatan, a shiga uzzura musu kan su janye. A ganina, wannan kuskure ne. Don haka, yajin aikin da malaman jami’a ke cikin a halin yanzu, ba na goyon bayan su janye, har sai gwamnati ta biya bukatun da suka nema, musamman kasancewar ba bukatu ne na kashin kansu ba, na al’umma ne, ’ya’yan talakawa ne kuma za su ci gajiyar sa, yadda ruhin ilimi zai dawo, ’yan wasu kasashen su rika zuwa nan neman ilimi, maimakon mu mu rika fita nema wurinsu.