Yajin aikin malaman jami’a: Su janye ko su canja salo?1

An dauki lokaci mai tsawo da malaman jami’a ke cikin yajin aiki. Duk da cewa suna ta tattaunawa tsakaninsu da gwamnati amma abin ya ci tura, suna ci gaba da yajin aiki, dalibai na zaune dirshan a gidajensu. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace malaman su janye daga yajin aikin ko kuwa […]

Yajin aikin malaman jami’a: Su janye ko su canja salo?1
Yajin aikin malaman jami’a: Su janye ko su canja salo?1

An dauki lokaci mai tsawo da malaman jami’a ke cikin yajin aiki. Duk da cewa suna ta tattaunawa tsakaninsu da gwamnati amma abin ya ci tura, suna ci gaba da yajin aiki, dalibai na zaune dirshan a gidajensu. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace malaman su janye daga yajin aikin ko kuwa su canja salo? Wakilanmu sun tattauna da al’umma kan haka kuma ga ra’ayoyinsu kamar haka:

Malaman jami’a su ci gaba da yaji
– Babatunde Opayemi
Babatunde Opayemi: “Yajin aikin da malamai ke yi, a nawa ra’ayin ya yi daidai, domin haka zai kara fito da irin gwamnatin da muke da ita sarari kuma ’yan Najeriya za su san cewa shin gwamnatin nan mai jin kukan jama’a ce ko kuwa harkar gabanta ta dame ta? Wannan zai sa mutanen Najeriya su koyi darasi idan sun zo zabe su san wane irin mutane za su zaba. Domin abin da wadannan malaman ke nema sai ka tarar mutum guda na iya kwashe su kuma ya zauna lafiya. Babban abin da kawai ke damu na shi ne, dalibai su ne ke shan wannan wahalar amma wani dadin sai an wahala, domin idan ba yajin aiki ba gwamnatin Najeriya ba ta jin kowace irin magana kuma ni a tawa fahintar, ban san wata hanya da za su bi ba da ta wuce wannan domin ko magabata sun shiga maganar sau tari amma hakan bai yi tasiri ba. Don haka su ci gaba da wannan yajin aikin har sai gwamnati ta gaji tasaurare su.”

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno