Yajin aikin malaman jami’a: Su janye ko su canja salo?2

An dauki lokaci mai tsawo da malaman jami’a ke cikin yajin aiki. Duk da cewa suna ta tattaunawa tsakaninsu da gwamnati amma abin ya ci tura, suna ci gaba da yajin aiki, dalibai na zaune dirshan a gidajensu. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace malaman su janye daga yajin aikin ko kuwa […]

Yajin aikin malaman jami’a: Su janye ko su canja salo?2
Yajin aikin malaman jami’a: Su janye ko su canja salo?2

An dauki lokaci mai tsawo da malaman jami’a ke cikin yajin aiki. Duk da cewa suna ta tattaunawa tsakaninsu da gwamnati amma abin ya ci tura, suna ci gaba da yajin aiki, dalibai na zaune dirshan a gidajensu. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace malaman su janye daga yajin aikin ko kuwa su canja salo? Wakilanmu sun tattauna da al’umma kan haka kuma ga ra’ayoyinsu kamar haka:

Ya kamata malaman su janye yajin aikin – Yunusa Abdullahi

Malam Yunusa Abdullahi: “Ni dai a ra’ayina, ya kamata malaman jami’a su janye wannan yajin aiki da suka dauki lokaci suna yi saboda dalilaina kamar haka: Na farko, su duba halin da dalibai suke ciki, su tausaya masu. Tsawaita yajin aikin nan zai kawo cikas ga karatunsu, kuma mafi yawa ’ya’yan talakawa ne ke jami’o’in nan. Na biyu, ya kamata malaman su nuna kishin kasa, su yi hakuri da abin da gwamnati take musu, su dawo bakin aiki don taimakon al’umma. Na uku, ya dace malaman su duba irin koke-koken da al’umma ke musu kan wannan, idan suka dawo aiki sai su tsaro wata hanyar da za su bi domin ganin gwamnati ta biya musu bukatunsu amma dai a yanzu ya kamata su dawo aiki.”

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno