Yajin aikin malaman jami’a: Su janye ko su canja salo?3

An dauki lokaci mai tsawo da malaman jami’a ke cikin yajin aiki. Duk da cewa suna ta tattaunawa tsakaninsu da gwamnati amma abin ya ci tura, suna ci gaba da yajin aiki, dalibai na zaune dirshan a gidajensu. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace malaman su janye daga yajin aikin ko kuwa […]

Yajin aikin malaman jami’a: Su janye ko su canja salo?3
Yajin aikin malaman jami’a: Su janye ko su canja salo?3

An dauki lokaci mai tsawo da malaman jami’a ke cikin yajin aiki. Duk da cewa suna ta tattaunawa tsakaninsu da gwamnati amma abin ya ci tura, suna ci gaba da yajin aiki, dalibai na zaune dirshan a gidajensu. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace malaman su janye daga yajin aikin ko kuwa su canja salo? Wakilanmu sun tattauna da al’umma kan haka kuma ga ra’ayoyinsu kamar haka:

Na goyi bayan ci gaba da yajin aiki
– Yusuf Yahaya

Alhaji Yusuf Yahaya: “A gaskiya muna goyan bayan yajin aikin nan da malaman jami’o’in kasar nan suke yi. Saboda abubuwan da ake yi a kasar nan kan harkokin ilmi
sun yi matukar munana. Wannan abin bakin ciki ne a kasar nan, a ce gwamnati ba za ta iya tafiyar da jami’a ba, har sai an tura dalibanmu zuwa kasashen Malesiya da Ghana karatu. Malaman jami’ar nan fa, ba suna magana ne kan karin albashinsu ba, suna magane ne kan samar da kayayyakin aiki ne a jami’o’in kasar nan. A yanzu a kasar nan akwai daliban da suke karatun likitanci a jami’o’in nan, wadanda idan sun kammala karatunsu ba za su iya rubuta wa marasa lafiya magani ba. Saboda rashin kayayyakin aiki a jami’o’in kaasar nan.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno