Yajin aikin malaman jami’a: Su janye ko su canja salo?4

An dauki lokaci mai tsawo da malaman jami’a ke cikin yajin aiki. Duk da cewa suna ta tattaunawa tsakaninsu da gwamnati amma abin ya ci tura, suna ci gaba da yajin aiki, dalibai na zaune dirshan a gidajensu. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace malaman su janye daga yajin aikin ko kuwa […]

Yajin aikin malaman jami’a: Su janye ko su canja salo?4
Yajin aikin malaman jami’a: Su janye ko su canja salo?4

An dauki lokaci mai tsawo da malaman jami’a ke cikin yajin aiki. Duk da cewa suna ta tattaunawa tsakaninsu da gwamnati amma abin ya ci tura, suna ci gaba da yajin aiki, dalibai na zaune dirshan a gidajensu. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace malaman su janye daga yajin aikin ko kuwa su canja salo? Wakilanmu sun tattauna da al’umma kan haka kuma ga ra’ayoyinsu kamar haka:

Kada malamai su ci gaba da yaji
– Abdulkadir Mustapha
Abdulkadir Mustapha: “Gaskiya ci gaba da yajin aikin da malaman jami’a ke yi, ban goyi bayan su ba, domin yara ko kuma in ce dalibai suke shan wahala kuma cikin daliban nan akwai ’yan uwansu. Wasu ma akwai ’ya’yansu kuma sau nawa suke yajin aiki amma har wa yau ba su samu biyan bukata ba, daga lokacin da suka fara wannan yajin aikin kawo yanzu, dalibai sun yi hasara, wanda kuma ba za su samu abin da ya maye gurbin wannan hasarar ta lokacin da suka yi ba har abada. Fatana shi ne, Gwamnatin Tarayya ta dubi wannan lamari da idon basira, su zauna da malaman jami’ar nan su sulhunta, kowa bai samun yadda yake so kuma Najeriya ba ta masu mulki ba ce su kadai haka su ma malaman jami’a, su yi la’akari da cewa Najeriyar ba ta su ba ce su kadai, domin kowane dan Najeriya na da rawar da zai taka domin ci gaban kasar nan.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno