Yajin aikin malaman jami’a: Su janye ko su canja salo?5
An dauki lokaci mai tsawo da malaman jami’a ke cikin yajin aiki. Duk da cewa suna ta tattaunawa tsakaninsu da gwamnati amma abin ya ci tura, suna ci gaba da yajin aiki, dalibai na zaune dirshan a gidajensu. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace malaman su janye daga yajin aikin ko kuwa […]
An dauki lokaci mai tsawo da malaman jami’a ke cikin yajin aiki. Duk da cewa suna ta tattaunawa tsakaninsu da gwamnati amma abin ya ci tura, suna ci gaba da yajin aiki, dalibai na zaune dirshan a gidajensu. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace malaman su janye daga yajin aikin ko kuwa su canja salo? Wakilanmu sun tattauna da al’umma kan haka kuma ga ra’ayoyinsu kamar haka:
Yajin aikin shi ya fi zama daidai – Sarkin Aska
Malam Ishak danjuma Sarkin Askan Jos: “A tsarin ilmi irin na kasashen duniya, an yi wa Najeriya fintinkau, domin a wasu kasashe irin kasafin kudin da ake yi wa harkokin ilmi shi ne yake kan gaba. Amma a nan Najeriya gwamnati ba ta damu da harkokin ilmi ba. Za ka ga ana ciwo bashin kudade daga kasashen waje da sunan bunkasa harkokin ilmi amma sai ka ga an karkatar da wadannan kudade.
“A lokacin gwamnatin tsohon Shugaban kasa marigayi Janar Sani Abacha, an ware bangare na musamman don tallafa wa harkokin ilmi a kasar nan. Kuma an yi aiki da kudaden da aka ware a lokacin, wajen samar da kayayyakin aiki a jami’o’in kasar nan.