Yajin Aikin Malaman Jami’o’i

Ina son Editan wannan Jarida ya taimaka ya ba ni fili in isar da sakona ga daukacin shugabannin wannan kasa ta mu. Ban ga amfanin tausasa harshe ga shugabannin mu, dan ba za su taba gyarawa ba. Meye amfanin yi musu nasiha? Meye damuwar su da Jami’o’in kasar nan? Ina ruwan su kuwa? Tunda sun […]

Yajin Aikin Malaman Jami’o’i
Yajin Aikin Malaman Jami’o’i

Ina son Editan wannan Jarida ya taimaka ya ba ni fili in isar da sakona ga daukacin shugabannin wannan kasa ta mu. Ban ga amfanin tausasa harshe ga shugabannin mu, dan ba za su taba gyarawa ba. Meye amfanin yi musu nasiha? Meye damuwar su da Jami’o’in kasar nan? Ina ruwan su kuwa? Tunda sun kwashi yayan su sun kai kasar waje. Su kuma malaman meye damuwar su tunda suna nan cikin gidajen Gwamnatin da suke yi wa yaji? Ba su biyan kudin wuta ballanta na na haya. Me yasa ba za ku bar har gidajen ba? Kunya kam saura ta lahira, amma ta duniya an dade da yin ta. Daga Bashar Bello Linguist Jihar Sakkwato. 07063691636.

Sakonnin waya

Sakon Ramadana
Asslaamu alaikum. Aminiya ina mika sakon taya murnar zuwan watan Ramadan ga al’ummar Musulmi. Allah Ya karbi Ibadunmu. Daga Murtala Musa Kaigama 08036859873.

Sakon Ramadana
Asslaamu alaikum Manzon Allah (SAW) ya ce, kada ku yi wa juna hassada, kuma kada ku yi wa juna kyashi; kada ku yi wa kiyayya; kada ku yi wa juna rudi a ciniki; kada waninku ya yi ciniki a kan cinikin waninsa. Ku zama bayin Allah ’yan uwan juna. Musulmi dan uwan Musulmi ne, kada ya zalunce shi, kuma kada ya tabar da shi; kada ya wulakanta shi. Tsoron Allah a nan yake. Ya fadi haka har sau uku, yana nuna kirjinsa. Ya isshi sharri ga dan uwansa ya ya wulakanta Musulmi jininsa da dukiyarsa da mutuncinsa haramun ne. Allah Ya ba mu dace a Ramadan. Daga Izzatu A. Rashid

Jinjina ga Aishatu dahiru Binani
Yabon gwani ya zama dole, Aminiya ku isarmin da sakon jinjina ga yar majalisan wakilai, mai wakiltar Yola ta kudu da Yola ta Arewa da mazabar Girei a majalisan wakilai, Hajiya Aishatu dahiru Binani mace mai kamar maza, agaskiya muna dada godewa wannan baiwar Allah. Ganin yadda take share wa talakawa kukansu, ko ina ka za ga cikin mazabunta ta tona rijiyar burtsatse (borehole), mai amfani da hasken rana. A makon da ya gabata ne ta raba wa matan mazabunta keke napep, don kawar da talaucin. Ta raba wa yaran talakawa jakukkuna, don inganta karatun ’ya’yan talakawa. Allah Ya saka wa wannan baiwar Allah da Aljannatul Firdausi. Daga Faisal Muhammed Girei, Yola Jihar Adamawa. [email protected]

Sudan ta Kudu ta cika shekara 2
Allah sarki shekara kwana inji masu iya magana.A yau inason inyi magana akan cikar kasar Sudan ta Kudu shekaru biyu cif-cif da kasar ta yi da samun ‘yancin kai daga kasar Sudan. A nan ina son in yi kira ga al’ummar kasar da su kara zage damtse wajen yi wa kasar ayukkan cigaba, tare da yakar duk wani abu dake yunkurin dakushe cigaban kasar. Daga AbdulMalik Sa’idu Mai Bitredi, Tashar Bagu gusau

A kula da bakin haure
Korar bakin haure da Gwamnatin Tarayya ta Najeriya ke yi a halin yanzu, bai dace ba,  kuma zalunci ne. Domin korar takan shafi talakkawa ne masu neman na Maggi, wadanda suka hada da masu saida ruwa da shayi da sigari da masu aikatau wurin masu tuwo-tuwo da masu tura baro.da sauran su. Ana Najeriya muna da bakin haure bila adadin masu aikin gwamnati, amma su dokar ba ta shafe su ba, saboda suna da uwa a bakin murhu.To ya dai kamata aji tsoron Allah. Daga Haruna Muhammad Katsina.

Fatan alheri ga Aminiya
Lokaci ya yi da yakamata a dada yi maku addu’o’i na fatar alheri. Saboda haka ne na ga ya dace na mika tarin dimbin miliyoyin godiyarmu dangane da huɓɓasa tare da namijin kokarin da jaridar Aminiya ta yi tun lokacin kafuwarta wanda ko shakka babu ya samar shirye-shirye da suka hada da na ilmantarwa, tare da nishadantarwa da bai wa kowa dama ba tare da nuna bambancin siyasa ba ko na addini.  Allah ta’ala ya kara shige maku a gaba dare ko rana,ya kuma kara fasaha da hikima da zalaka fiye da kowace kafar yada labarai a duniya.
DagaIsah Kwafsi Asarara Shagari, Sakkwto 08087436699.

Ga Majalisar kasa
Majalisun Najeriya za su koma bakin aiki bayan hutu da suka je, Allah Ya sa abubawan da za su tattauna ya kawo ci gaba a kasar nan, musamman ma a lokacin da kasar ta dauki wani sabon salo dangane da karin wa’adi na shekaru 6 ga shugaban kasa da kuma gwamnoni idan aka yi la’akari da yadda kasar nan take na yawan canja kudin tsarin mulkin kasar. Daga Ishak Abdullahi dan Rimi Bena.

Ga Shugaban karamar Hukumar Kware
Wasika zuwa ga Shugaban karamar Hukumar mulki ta Kware, Alhaji Abubakar dan Masanin Zamau game da ayyukan da yake yi wa jama’arsa, mu mutanen Zamau muna yi maka fatan alheri. Sai dai a cikin wasu ayyukan da kake yi akwai gyara, saboda ka yi mana titi a garin Zamau, amma ba inda aka yi kwalbati. Ko kai san in babu kwalbati, to ba titi ken an. A dauki matakin gaggawa na gyarawa. Daga Umar Abaji Zamau Alelu. 08037494622.

jinjina ga Solomon Dalung da Lamido Sanusi
Salam Aminiya jinjina ga Barista Solomon Dalung da Sanusi Lamido Sanusi. Ya kamata mu auna maganganun da suke yi; Magana ce ta masu karatu d ailimi, bat a masu zallar karatu. Ba gaskiya day a cedaga ki sai? Daga Umar 08027648800.

Ga dan Majalisa Datti Babawo
Salam Aminiya ina so ku mika  sakon ga Hon  Garba Datti Babawo mai wakiltar Sabon-gari. Mun zabe shi, amma ba mu shaida komai  a wakilcin sa ba. To a dai rika tunawa da mutuwa. Daga Rabi’u Salihu Buhariyya Sak. 08036859012.

Ga ’yan sanda
Aslam alaikum, Aminiya mai farin jini wai meyasa police suke shiga aikin da ba na su ba? Sai a Najeriya meye hadinsu da Number. Daga Shakcy San GRA. 08133692601.

Mawaka a ji tsoron Allah
Salam Mawakan addini ku ji tsoron Allah, ku daina amfani da son ra’ayinku ko wani dalili boyayye, kuna saba wa Allah. Don addini ba ra’ayi ba ne, har ta kai kuna yi wa Allah kishiya, ta hanyar fifita wani da ba shi siffofin Allah a cikin wakokinku Ni ba kowa ba ce, amma a yadda na sani Allah Shi ne Lamyalid walam yu lad. Kuma shi Ya halicci komai da kowa, babu laifi mafi girma sama da shirka; kuma duk mai shirka kafirine! Sanin daidai sai Allah. Kuma babu wanda zai hana kowa bin ra’ayinsa. A daina rarraba kan al’umma da hankalinsu da sunan addini. Lallai masu yi su ji tsoron Allah, a kiyaye dokokin Allah. Allah Ya sa mu dace. Amin. Daga Hafsat 08080238631.

Talaka na wahalar mota a Abuja
Aminiya ina so in dan yi karin bayani game da harkokin sufuri da ke garin Abuja, wanda Ministan Abuja ya kirkiro da shi, to gaskiya gwamnati tana yin abu wanda idan dan Adam ya zauna da kyau ya yi tunani kuma ya hanga gwamantin kasar nan tana da matsala babba. Game da harkokinh yau da kullum, ta yadda talaka ke cikin wani hali. Ya kuka duba a cikin Abuja an hana kabu-kabu, to wannan akwai basira a kan wannan saboda ’yan kabu-kabu wani lokaci ana kashe su a banza, saboda yanayin tsarin titi da ke Abuja ba kowa yasan dokar hanya ba; komai iliminka kai ilimi ma da ya kare balle a ce wanda ba ya da ilimi, kuma ya shigo birni yana kabu-kabu, to a nan shi ne ga shi yau kuma an hana bas-bas su yi zirga-zirga a cikin Abuja. Daga Ilyas Idris Fahad Suleja 08030777041.

Allah Sarki Katsinawa
Wai ’yan siaysar Nijeriya sun ce garinmu akwai talauci duk da noma d akiwo d amuke das hi ga mu da manya-manyan attajirai. Anya ana yi wa Katsinawa adalci kuwa? Koko don a bata wa Mai girma Gwamna Ibrahim Shehu Shema da Jiharmu suna. Daga Nura GGK Fatakwal 08064411055.