Yajin Aikin NLC ya hana Tantance Kwamishinoni a Gombe
Yajin aikin NLC ya tilasta wa Majalisar Jihar Gombe dage tantance kwamishinonin jihar da gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya tura sunayensu.
Yajin aikin Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ya tilasta wa Majalisar Dokokin Jihar Gombe dage tantance kwamishinonin jihar da gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya tura sunayensu.
Da farko, a safiyar Talata Majalisar ta shirya fara tantance mutum 17 da gwamnan ya mika sunayensu a matsayin kwaminishinoni, bayan tsawon lokaci da ta ki tantance su.
- Muna fatan kulla yarjejeniya da ECOWAS — Sojin Nijar
- Sojoji sun kashe masu garkuwa da mutane 6 a Filato
Shugaban Majalisar, Abubakar Muhamamd Luggerewo, ne ya fitar da sanarwar dage zaman Majalisar don fara tantace hwamishinonin har sai bayan yajin aikin gargadin na kwana biyu, zuwa ranar Alhamis 7 da Juma’a 8 ga watan Satumba 2023.
Majalisar dai ta dauki sama da kwanaki 38 sunayen na gabanta ba tare da tantance su ba, wanda ake tunanin takun saka tsakaninta da gwamnan jihar ne ya haifar da hakan.