Yajin ma’aikatan mai ya jawo mugun karancin fetur a Legas da Kaduna
Yajin aikin jan kunne da ma’aikatan bangaren man fetur suka kira ya jawo mugun karancin mai a jihohin Legas da Kaduna, yayin da aka kasa cimma matsaya a ganawar da suka yi da Ministan kwadago a daren shekaranjiya Laraba.kungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Gas ta kasa (NUPENG) ta fara yajin aikin jan kunne ne a […]
Yajin aikin jan kunne da ma’aikatan bangaren man fetur suka kira ya jawo mugun karancin mai a jihohin Legas da Kaduna, yayin da aka kasa cimma matsaya a ganawar da suka yi da Ministan kwadago a daren shekaranjiya Laraba.
kungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Gas ta kasa (NUPENG) ta fara yajin aikin jan kunne ne a ranar Litinin kan zargin rashin adalci ga ma’aikata da wasu manyan kamfanonin mai suke yi a kasar nan.
Shugaban kungiyar NUPENG Kwamared Igwe Achese ya shaida wa manema labarai a ranar Talata cewa wajibi ne gwamnati ta tabbatar masu ruwa da tsaki a fannin mai suna bin ka’idoji kan yarjejeniyar daukar aikin wucin-gadi da tabbatar da su cikakkun ma’aikata.
A joint stakeholders meeting of gobernment, oil companies and unions is edpected to hold today on how to resolbe the crisis.
Achese, wanda ya yi jawabi a wurin aron hadin gwiwa da kungiyar Manyan Ma’aikatan Man Fetur da Gas ta Najeriya (PENGASSAN), ya ce NUPENG za ta gudanar da taron Majalisar Zartarwarta bayan taron manema labaran domin daukar maaki na gaba.
kungiyar ta shawarci Gwamnatin Tarayya ta yi hobbasa wajen yakar satar mai, inda ta nuna akwai bukatar a kara wa Rundunar Sojan Ruwa kudin gudanar da ayyukan yadda ya kamata. Ya ce a sanya NUPENG da PENGASSAN a cikin kwamitin da aka kafa kwanan nan domin yaki da satar mai.
Yajin aikin ya jawo karancin mai, inda akle ganin dogayen layuka a gidajen mai tare da tashin farashin shiga motoci da kimanin kashi 50 cikin 100 a Legas da Kaduna.
A Legas NUPENG ta umarci masu sayar da mai a gidajen man fetur su daina sayar da man ga jama’a a wani bangare na yajin aikin jan kunnen.
Tashohin mota da dama sun cika da fasinjoji a sassan kasar nan, yayin da ake ganin bas daidaku a kan tituna.
A Kaduna masu motocin hawa suna sayen galan fetur kan Naira dubu daya kamar yadda Aminiya ta gano, yayin da gidajen maid a dama suka ki budewa.
has directed filling station attendants in the state to stop selling petroleum products to customers as part.
Wakilnmu ya lura jami’an kungiyar NUPENG suna sintiri domin tabbatar ana gudanar da yajin aikin a gidajen man.
“Muna sayar da galan kan Naira dubu daya, amma zan iya sayar maka kan Naira 800. Wannan ne lokaci na farko da wasunmu suka fara wannan harka. Muna amfani da yajin da NUPENG ta kira ne domin samun kudi,” inji wani dan bumburutu.
Rahotanni daga jihohin Ekiti da Katsina da Sakkwato da Ogun da Bauchi da kuma Abiya sun ce al’amura suna nan kamar yadda suke, sai dai mutane suna taka-tsantsan domin kada a yi musu ba-zata, ta yadda al’amura ba za su tabarbare ba.