Yajin malaman jami’o’i: ASUU ta ce ba wata bukata da gwamnati ta biya
Shugaban kungiyar Malaman Jami’o’i ta kasa (ASUU) Kwamared Nasir Fagge ya ce babu wata bukatar kirki da Gwamnatin Tarayya ta biya da zai sa malaman su janye yajin aikin da suka fara a ranar Talatar da ta gabata.Kwamared Fagge ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da Aminiya shekaranjiya Laraba, inda ya ce kuskure ne a […]

Shugaban kungiyar Malaman Jami’o’i ta kasa (ASUU) Kwamared Nasir Fagge ya ce babu wata bukatar kirki da Gwamnatin Tarayya ta biya da zai sa malaman su janye yajin aikin da suka fara a ranar Talatar da ta gabata.
Kwamared Fagge ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da Aminiya shekaranjiya Laraba, inda ya ce kuskure ne a ce kungiyar ta ki dakatar da yajin duk da an biya mata wasu bukatunta.
Ya ce, “A kan me gwamnatin ta biya bukatar? Yarjejeniyarmu ta kunshi abubuwa tara, kuma an sanya hannu kan takardar yarjejeniyar fahimtar juna a ranar 21 ga Janairun bara; idan ka biya bukata daya ko biyu, a kan wanne ne gwamnati ta biya bukatar?”
Lokacin da Aminiya tta nemi ya yi karin haske kana bin da aka yi musu tayi, Fagge ya ce, “Ku tambayi Ministar a kan wane batu ne ta biya bukata ko tayin.”
Da yake bayani kan dalilin shiga yajin, shugaban ya ce, kungiyar tta yanke shawarar shiga yajin aikin ne, saboda malaman jami’o’in ba za su ci gaba da “yaudarar kawunansu cewa suna aiki ba, alhali al’amura suna ttabarbarewa.”
Ya ce, karuwar lalacewar jami’o’in ce ta tilasta kungiyar fara yajin, saboda Gwamnatin Tarayya ba ta nuna wani katabus don magance matsalar. “Shawara ce mai daci ka kira yajin aiki, domin mu ma iyaye ne. A jami’o’inmu yanzu za ka iske dalibai 12 a cikin daki daya kuma dukkansu suna amfani da risho 12 wajen girki a lokaci guda. Babu gine-gine ko kayayyakin aiki a jami’o’in, baa gudanar da ayyukan bincike. Don haka maimakon mu rika yaudarar kanmu cewa muna aiki, muna ganin shawara mafi dacewa mu yi wa kanmu kiyamul laili don ceto ’ya’yanmu masu zuwa. A matsayinsu na shugabannin gobe, sun cancanci su samu nagartaccen ilimi,” inji shi.
Tuni yajin aikin malaman ya dakatar da komai a kusan mafi yawan jami’o’in kasarn nan.