Yajin aiki: Mashawarcin Shugaban Kasa kan tsaro ya ba NLC hakuri
Nuhu Ribadu ya ce an kama bata-garin da suka lakada wa shugaban NLC na Kasa duka kawo-wuka a Imo
Mai ba wa Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, ya ba wa Kungiyar Kwadago (NLC da TUC) hakuri tare da neman su janye yajin aikin da suka fara.
Takardar ban hakurin Gwamnatin Tarayyar da Ofishin NSA ya fitar ta hannun daraktan yada labaransa, Zakari Mijinyawa ta sanar da cewa jami’an tsaro sun yi nasarar kamo mutanen da ake zargi da dukan Shugaban NLC na Kasa, Joe Ajaero.
Sanarwar ta kara da cewa tuni jami’an tsaro suka fara gudanar da bincike kan lamarin domin gurfanar da wadanda ake zargin.
Nuhu Ribadu ya yi Allah wadai da harin da aka kai wa shugaban na NLC, wanda ya ci ya saba wa tsarin dimokuradiyya da ma ’yancin dan Adam.
Don haka ya ce ba za a bar wadanda suka yi wannan aika-aika su sha ba, sai sun fuskanci hukunci.
Sai dai ya bayyana cewa yajin aikin da kungiyar NLC da takwararta ta TUC suke jagoranta a halin yanzu ya jefa al’ummar kasa cikin karin matsi.
A ranar 1 ga watan Nuwamba ne wasu bata-gari suka laka da wa Mista Ajaero duka kawo-wuka a Owerri, babban birnin Jihar Imo.
NLC ta zargi ’yan sanda da Gwamna Hope Uzodinmna da ke takun saka da Ajaero, amma kowannensu ya nesanta kansa da abin da ya faru.
A kan haka ne NLC ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta dauki matakin da ya dace kan lamarin, ta kuma yi barazanar shiga yajin aikin da ta fara a ranar Talata.