…Yakamata ku bar ni in huta -Stephen Keshi
Tsohon kocin kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles Stephen Keshi ya roki ’yan Najeriya da ke yawan aika masa sakonnin tambayoyi akan al’amurran da suka shafi Super Eagles su kyale shi haka ya huta tun da an kore shi. Ya ce maimakon su aika masa wata tambaya, kamata ya yi su aika zuwa Hukumar […]
Tsohon kocin kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles Stephen Keshi ya roki ’yan Najeriya da ke yawan aika masa sakonnin tambayoyi akan al’amurran da suka shafi Super Eagles su kyale shi haka ya huta tun da an kore shi. Ya ce maimakon su aika masa wata tambaya, kamata ya yi su aika zuwa Hukumar NFF ko kuma kocin da ke kula da kungiyar a halin yanzu.
Kocin ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar daga Amurka inda yanzu haka yake zaune tare da iyalinsa.
Ya ce duk mai bukatar yin wata tambaya, to yana ba shi shawarar ya aikata zuwa ga Mataimakin kocin Eagles na yanzu Abdullahi Yusuf.
“Ina rokon ’yan Najeriya su bar ni don na huta da iyalina a Amurka. Abin da kawai nake bukata shi ne na huta tare da iyalina, kuma na kawar da hankalina daga duk wani abu da ya faru da ni a kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles. Ina so jama’a su sani daga yanzu babu abin da ya hada ni da kungiyar, kuma zai fi dacewa ku aika tambayoyinku ga mai rikon kwaryar kungiyar Abdullahi Yusuf ko kuma ga duk wanda yake da alhakin tafiyar da harkokin kungiyar”, inji Keshi.
A ranar Asabar da ta wuce ne dai Hukumar NFF ta sallami Stephen Keshi daga kungiyar a matsayin koci. Kuma a yau ne ake sa ran hukumar za ta sanar da sabon kocin kungiyar. Jim kadan da sallamarsa ne ya fice Najeriya zuwa Amurka inda yake zaune da iyalinsa.