Yakamata Wamakko ya san kalaman da zai rika fada – Sanata Wali

Sanata Abdallah Wali dan takarar Gwamnan Jihar Sakkwato a Jam’iyyar PDP a zantawarsa da manema labarai ya tabo kalaman da Gwamna Wamakko ya furta kan zabe mai zuwa da sauransu:  Aminiya: Tun lokacin da aka dage zabe a kasar nan ka ci gaba da zagayawa domin neman jama’ar Jihar Sakkwato su zabe ka, yaya za […]

Yakamata Wamakko ya san kalaman da zai rika fada – Sanata Wali
Yakamata Wamakko ya san kalaman da zai rika fada – Sanata Wali

Sanata Abdallah Wali dan takarar Gwamnan Jihar Sakkwato a Jam’iyyar PDP a zantawarsa da manema labarai ya tabo kalaman da Gwamna Wamakko ya furta kan zabe mai zuwa da sauransu: 

Aminiya: Tun lokacin da aka dage zabe a kasar nan ka ci gaba da zagayawa domin neman jama’ar Jihar Sakkwato su zabe ka, yaya za ka kwatanta karbuwarka da jam’iyyarku zuwa yanzu?
Wali: Ba abin da zan ce sai wannan jinkiri ya haifar mana da nasara dukkanmu ’yan Jam’iyyar PDP, mun kammala zagayenmu a dukkan kanannan hukumomi 23 sai kai muka ji sanarwa hukumar zabe ta dage zabe sai bayan mako shida. A lokacin ba mu ji dadi ba don muna ganin kamar zai kawo mana cikas bayan haka ne muka yi ta samun sakonnin goyon baya da fatar alheri, wannan ya ba mu kwarin gwiwa muka ci gaba da kamfe. Gaskiya wannan karin nasara ne a wurinmu, domin mutane sun kara fahimtarmu da goyon bayanmu da ya sanya mu cikin farin ciki sosai. Wannan ratar ne da aka samu ta ba mu damar sanya wa takardar zaman lafiya hannu da hukumomin tsaro suka fito da ita, ni banyar da tashin hankali ko rigimar siyasa ba, kuma idan na zama Gwamnan Sakkwato zan magance wannan domin sakaci ne na hukuma, za mu yi bincike sosai mu inganta kotunanmu don yanke hukuncin gaskiya, yanzu ka tafi gidajen yari ba za ka samu mutanen da aka tsare ba don rigima da tashin hankali lokacin siyasa, abin da ba zan yarda da shi ba duk wani mutum da aka kama da tada zaune-tsaye, shi da wanda ya sanya shi ba zan saurara musu ba, dole doka ta yi aikinta a kansu. Ina ba ka tabbacin siyasar 2019 a Jihar Sakkwato babu siyasar tada hankali da jikkata mutane, saboda duk masu yi suna gidan yari, hakan zai sa wani ba zai yi sha’awar yi ba. A wannan dagewar da aka yi ne muka fahimci ya zame mana wajibi mu canja gwamnatin Wamakko don ba ta san abin da za ta yi da kudin al’ummar jiha ba, ka tafi kauye da karkara misali karamar Hukumar Sabon Birni akwai gadar da ke shirin faduwa wadda mutane suka daina hawa samanta ta hada kauyuka da dama, a kauyen Kamarawa kuma akwai gadar da ta fadi kasa warwas ta raba mutanen da na kauyen Shinkafi, a Kuci ma akwai hanya kusan kilomita 25 da aka kasa aiwatar da ita duk dan kauyen da yake son ya zo hedkwatar karamar hukumarsa ta Kebbe sai ya je Jega ya zagayo ya ci kilomita fiye da 60, inda ake da wadannan ayyukan aka abar su aka tafi wurin lalata kudi ga rushe ginin gidan gwamnati da yake lafiya lau don yin sabo da aka kasa kammalawa da yin sabuwar sakatariya ita ma ba a kammalata ba. Wannan ba gwamnati ba ce da ta san abin da za ta yi na amfanin jama’a ba don babu wani shiri a tsare.
Aminiya: Gwamna Aliyu Magatakarda Wamakko ya yi zargin cewa wannan zaben da za a yi kun yi tattaunawar sirri a gidan Bafarawa kun shirya magudi da fadin sakamakon zabe tun kafin hukumar zabe ta sanar, yaya lamarin yake?
Wali: Ba ni ne ya kamata in amsa wannan tambayar ba domin muna da hukumar zabe mai cin gashin kanta, ita ce ke da alhakin gudunar da zabe da fadin sakamakonsa, yaya za a yi wani can daga wata jam’iyyar siyasa ya fadi sakamakon zabe, wannan wulakantar da hukumar zabe ne ya yi, na nuna ba ta yin aikinta. Ya kamata mutane su fahimci yanayin da ake ciki yanzu ya riga ya san ya fadi zabe da dukkan alamun da yake gani don haka ne ya fito da wannan dasisar bayan zabe ya gaya wa magoya bayansa “Ai na fada muku tun farko sun shirya zabensu” don haka wannan magana ce da ba ta da tushe ko makama, domin gidan da ya ce an zauna a lokacin da yake fadin hakan mai gidan yana Saudiyya kuma ya ce da shi aka yi zaman yaya mutumin da ke kasar waje kuma a yi zama da shi a nan Sakkwato? Wannan maganar ba gaskiya ba ce, jam’iyyarmu ba ta da hurumin fadin sakamakon zaben kasa baki daya. Gwamna Wamakko ya kamata ya san irin kalaman da zai furta a matsayinsa na shugaba a Najeriya don gudun haddasa rigima. Irin wadannan abubuwa ne suka sanya muke son canja wannan gwamnati don ceto al’umma daga fadawa cikin rashin tabbas.
Aminiya: Ka yarda da a-kasa-a tsare-a-raka?
Wali: Wannan salo ne na APC dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar ne ya zo da wannan salon a wasu zabe da suka gabata, in ka dubi wannan manufa ce ta kare kuri’a wadda mu a jam’iyyance mun dauki matakin kare kuri’armu domin Shugaba Jonathan ya ce ba wata kuri’a da ba za a kidaya ba, kan wannan ne hukumar zabe take kara inganta yanayin zabe ta hanyar zamanantar da shi, don abubuwan da za a yi
amfani da su ba a taba yi ba kamar na’urar tantance masu zabe, bai kamata a zo mana da wata damuwa ba domin dokar zabe ba ta ba ka damar in ka yi zabe ka tsaya ba, don kana da jami’i da jam’iyyarka ta sanya don kula da zabe ganin ba a yi wa jam’iyyarka sama da fadi ba.