Yakasai da Waku da Na’abba sun nemi goyon bayan IBB

Shugaban Kungiyar Shugabannin Arewa da Masu Ruwa d Tsaki ta NLSA, Alhaji Tanko Yakasai jiya ya jgoranci membobin tafiyar da kungiyar zuwa garin Mina don neman goyon bayan tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya, Shugaba Ibrahim Badamasi Babangida.   A tawagar shugaban akwai tsohon shugaban majalisar wakilai ta tarayya, Ghali Umar Na’abba da tsofaffin ministoci […]

Yakasai da Waku da Na’abba sun nemi goyon bayan IBB

Shugaban Kungiyar Shugabannin Arewa da Masu Ruwa d Tsaki ta NLSA, Alhaji Tanko Yakasai jiya ya jgoranci membobin tafiyar da kungiyar zuwa garin Mina don neman goyon bayan tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya, Shugaba Ibrahim Badamasi Babangida.
 
A tawagar shugaban akwai tsohon shugaban majalisar wakilai ta tarayya, Ghali Umar Na’abba da tsofaffin ministoci biyu na birnin tarayya na Abuja, Sanata Bala Muhammad da Mohammed Abba Gana da tsohon ministan ciniki, Alhaji Mustapha Bello da kuma Sanata Joseph Waku.
 
Sauran sun hada da tsofaffin ministocin ma’aikatar mata biyu, Hajiya Mrayam Inna Ciroma da Hajiya Zainab Maina da tsohon ministan tsarin kasa, Dokta Mohammed Shata da tsohon gwamnan jihar Neja, Dokta Babangida Aliyu.
 
Da yake jawabi, Alhaji Tanko Yakasai ya ce sun kafa kungiyar a ranar 10 ga watan Fabarairun shekarar 2018 don tunkarar bukatar bunkasar al’adu da ci gaban siyasar dukkan ’yan Arewa da kuma Najeriya baki daya.
 
Ya bayyana cewa kungiyar ta siyasa ce amma ba mai nuna son kai ba inda ya ce “Kofofin kungiyar a bude suke ga dukkanin ’yan Arewa duk da bambancin addini da kabila da kuma siyasarsu”.


Kofin Duniya: Jamus ta lallasa Curaçao da ci 7 a wasan farko

Mahaifinmu ba shi da ciwon suga – Ɗan Janar Rabe

Sojoji sun daƙile harin Boko Haram, sun ceto mutum 9 a Borno

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai