Yaki da annobar Ebola a Yammacin Afirka
Cutar Ebola mai saurin kisa, cuta ce da ke ci gaba da yaduwa a wasu kasashen yankin Yammacin Afirka wadda kuma ta yi sanadiyyar mutuwar mutum fiye da 500 a kasashen Guinea da Liberiya da kuma Sierra Leone tun farkon bullanta a watan Janairun bana.Matakan yaki da cutar da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta […]
Cutar Ebola mai saurin kisa, cuta ce da ke ci gaba da yaduwa a wasu kasashen yankin Yammacin Afirka wadda kuma ta yi sanadiyyar mutuwar mutum fiye da 500 a kasashen Guinea da Liberiya da kuma Sierra Leone tun farkon bullanta a watan Janairun bana.
Matakan yaki da cutar da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta dauka da kuma rahoton da ke cewa an sanmu bullarta a kasar Ghana duka suna nuni ne da yadda annobar ke ci gaba da yaduwa sannu a hankali. Tun da dadewa akwai labarin bullarta a yankin Tsakiyar Afirka musamman ma Jamhuriyar Tsakiyar Afirka da Uganda, inda daga can ne ma’aikatan lafiya suka bayyana cewa cutar ta fara bayyana ne a jikin wasu mutane da ke cin naman biri. Kodayake a yankin Yammacin Afirka musamman kasar Guinea, ana danganta ta ne da maciya naman jemage wanda nama ne da ake darajawa sosai a kasar.Wannan ya sa ba tare da wata-wata ba hukumomin kasar suka dauki matakin haramta cinsa.
Kamar yadda masana suka bayyana, alamomin cutar sun hada da yoyon jini da hararwa da gudawa da zazzabi mai tsanani da sauransu. kwayar cutar na kashe mutum tara cikin goma da suka kamu da ita. Kuma kawo yanzu ba ta da rigakafi ko magani, hakan ya sa matakin yaki da ita ya ta’allaka ga takaita yaduwarta. Shakka babu, annobar za ta kara haifar da kanfar kiwon lafiya a kasashen da ta bulla wadanda da ma can samar da ayyukan kiwon lafiya ke da wuya. Misali yajin aikin ma’aikatan lafiya a Najeriya saboda bukatar karin albashi wanda matakin ya jawo gurguncewar fannin lafiyar kasar. Takaddama tsakanin gwamnatoti da likitoci a kasashen yankin ba sabon abu ba ne.
Ya dace hukumomin kasashen da ake samun irin wadannan takaddamar da su warwaresu ba tare da bata lokaci ba saboda hakan zai taimaka wajen yaki da cutar Ebola. A fili yake cewa yaki da cutar na bukatar hadin gwiwar dukkannin kasashen yankin. Saboda fahimtar hakan ya sa a farkon wannan watan aka kira wani taro a kasar Ghana don fitar da matsaya kan magance bazuwarta. Kodayake an so a makara, taron ya dace da an yi shi ne tuntuni saboda a takaita yaduwar cutar a kasar Guinea, kasar da aka fara samun bullarta. Zai yi kyau idan shugabanni a yankin za su fiddo da sabbin dabarun yaki da cutar. Idan ana son taron ya cimma burinsa, wajibi ne a aiwatar da matsayar da ya fitar ba tare da wani tsaiko ba.
Hakazalika, wani mataki da zai taimaka wajen kawo karshen annobar shi ne, wayarwa da jama’a kai ta yadda za su iya gane alamominta da kuma matakan da ya dace su dauka idan sun ga hakan, wanda ciki harda sanar da hukumomi mafi kusa da su.
A farko-farkon bullar annobar, an samu yaduwarta kamar wutar daji saboda yadda take saurin kama wadanda suke jinyar masu dauke da cutar. Wannan ya sa shirin wayarwa da jama’a kai wajen kiyaye cudanya da masu fama da ita ko da kuwa ’yan uwan su ne na jini yake da matukar amfani. Har ila yau, ya dace kasashen da ta bulla su bude wasu cibiyoyi da za a dunga amfani da su wajen kebe masu fama da cutar domin magani.
A yanzu da ta tabbata cewa akwai cutar Ebola a yankin Yammacin Afirka kuma tana kashe rayuka, ya kamata a sanya cutar cikin sahun gaba na jerin cututtukan da ake neman maganinsu. Wannan na yin ishara da cewa sai an karfafa binciken kimiyya a fatan ganin an gano maganinta, kafin cutar ta ci gaba da daukar rayukan al’ummar yankin; matakin farko don ganin hakan ya tabbata shi ne kowacce kasa da ke yankin, ta baiwa bangaren lafiya isassun kudi a kasafin kudinta.