Yaki da Boko Haram: A kara ba jami’an tsaro goyon baya – Sheikh Modu Mustapha

Wani fitaccen malamin addinin Musulunci da ke Maiduguri a Jihar Borno, Sheikh Modu Mustapha ya bukaci jama’ar yankin Arewa maso Gabas da yakin Boko Haram ya daidaita su bai wa jami’an tsaro hadin kai da goyon baya ta yadda za a ci galaban yakin da ake yi da su. Shiekh Modu Mustapha ya bukaci haka ne […]

Yaki da Boko Haram: A kara ba jami’an tsaro goyon baya – Sheikh Modu Mustapha
Yaki da Boko Haram: A kara ba jami’an tsaro goyon baya – Sheikh Modu Mustapha

Wani fitaccen malamin addinin Musulunci da ke Maiduguri a Jihar Borno, Sheikh Modu Mustapha ya bukaci jama’ar yankin Arewa maso Gabas da yakin Boko Haram ya daidaita su bai wa jami’an tsaro hadin kai da goyon baya ta yadda za a ci galaban yakin da ake yi da su.
 Shiekh Modu Mustapha ya bukaci haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a garin Maiduguri a karshen makon jiya, inda ya ce, “Shiyyar Arewa ta Gabas ta fuskanci tsananin tsoro da firgici a lokacin da Boko Haram suke cin karensu babu babbaka, inda wannan bala’i ya shafi kowa, babu maganar makaranta ko kasuwanci ko balaguro, ko ma a natsu a yi ibada ko wani aiki na addini, har ana ganin babu mahalukin da ya isa ya hana ’yan Boko Haram yin abin da suke yi a wancan lokaci. Amma Allah cikin ikonSa Ya kawo mana sauki na zuwan wannan gwamnati ta Shugaba Buhari, inda aka kakkabe cin hanci da rashawa da son zuciya a wajen yaki da ta’addancin.”
Sheikh Modu Mustapha ya ce wadanda suka assasa Boko Haram sun yi nufin su raba kawunan ’yan Najeriya ne ta hanyar daga gaba a tsakanin Musulmi da Kirista, amma sai Allah ya ganar da mutane da wuri, “Don haka wajibi ne mu hadu mu bai wa jami’an tsaro cikakken goyon baya ta yadda za su ci nasarar yakar wannan mummunar akida ta kashe mutane babu gaira babu dalili. Duk da za a iya cewa an cin nasara a yakin da ake yi da su, to amma ya kamata mutanen da ake yin wannan abu dominsu su bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga jami’an tsaro a samu nasarar dakile wannan ta’addanci domin kuwa ba Musulunci suke yi ba. Musulunci bai koyar a yi haka ba kuma yana fushi da wanda yake yi, don haka sun yi hannun riga da Musulunci. Muna rokon jama’a su taimaka a yake su a bayan kasa domin suna so su rushe Musulunci ne,” inji malamin.
 Sheikh Mustapha, ya jawo hankalin gwamnati game da samar wa matasan sa-kai na Sibiliyan JTF aikin yi ta yadda za su kasance masu dogaro da kawunansu, “Wajibi ne gwamnati ta duba gudunmawar da matasan suka bayar wajen samar da ingantaccen tsaro, domin idan aka bar su kara-zube, ba a samar musu da aikin yi ba, to baya za ta haifar da mummunan sakamako ta yadda ba za a ci moriyar matasan ba. Don haka muna rokon gwamnati ta yi hobbasa wajen samar musu da aikin yi, akwai matasa akalla sun haura dubu 10 a garin Maiduguri da sun taka rawar gani a fatattakar Boko Haram, kuma a ce ba su da wani abin da zai dauke masu hankali bayan a baya sun san makami sun dauki makami akwai matsala. Don haka ina rokon Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Borno su yi kokarin samar wa daukacin matasan da suka bayar da hadin kai ga yaki da Boko Haram aiki,” inji shi.

Zazzaɓin Lassa ya kashe mutum 214 a Najeriya — NCDC

An kama masu garkuwa da mutane a Borno 

Rikicin ya kunno kai a Hukumar Alhazan Jihar Delta

Sojoji sun ceto mutane 5 da ISWAP ta sace a Harin Ngoshe