Yaki da Boko Haram: Muna gani a kasa – Gwamna Shettima

Aminiya: Mene ne dalilin kafa wannan kwamiti na manyan alkalan Arewaci?Gwamna Shetima: Mun taru ne a yau domin mu ga yadda za mu yi mu shawo kan irin matsalolin da ke damun Arewa musamman a fannin ayyukan ta’addanci da sace-sacen dabbobi da kuma yadda ake sace-sacen mutane domin a karbi kudi da sauransu. Dokar Final […]

Yaki da Boko Haram: Muna gani a kasa – Gwamna Shettima
Yaki da Boko Haram: Muna gani a kasa – Gwamna Shettima

Aminiya: Mene ne dalilin kafa wannan kwamiti na manyan alkalan Arewaci?
Gwamna Shetima: Mun taru ne a yau domin mu ga yadda za mu yi mu shawo kan irin matsalolin da ke damun Arewa musamman a fannin ayyukan ta’addanci da sace-sacen dabbobi da kuma yadda ake sace-sacen mutane domin a karbi kudi da sauransu. Dokar Final Kod da ake amfani da ita a yankin Arewa a yanzu ba ta tanadi hukuncin dukkan abubuwan da ke damunmu ba. Shi ya sa muka kafa wannan kwamiti domin ya shawo kan wadannan matsaloli.
Aminiya: Wannan ya shafi canja dokoki ke nen wanda hakan ke nuna dokokin Arewa sun tsufa?
Gwamna Shettima: Ai babu shakka sun tsufa kuma ya cancanta inda za a yi garar a ga cewa dukkan matsalolin da ke addabarmu an sha kansu.
Aminiya: Mene ne ainihin aikin kwamitin da aka kafa?
Gwamna Shettima: Babban aikinsu shi ne su binciko masu tallafa wa ’yan ta’ada da kuma iyaye masu ba da ’ya’yansu ana amfani da su a matsayin ’yan kunar bakin wake. Hakkin kwamitin ne ya samar da doka ko hukuncin da za a yi amfani fa shi a kan duk wanda aka kama da laifin yin hakan. Haka nan kamar yadda na fadi ne cewa aikinsu ne su duba batun satar shanu da sace-sacen mutane da sauran manyan laifuffuka da nufin yin gyara. Mun kuma ba su wa’adin wata biyu ne kawai su fito mana da rahoton yadda za a magance wadannan matsaloli a yankinmu na Arewa.
Aminiya: A baya an sha kafa kwamitoci musamman a kungiyarku ta Gwamnonin Arewa amma sai a ji shiru. A wannan karon akwai tabbacin za a yi amfani da abin da aka tattauna a kan sababbin dokokin?
Gwamna Shettima: Insha Allahu za mu sake yin taro a wata uku masu zuwa kuma da yardar Allah za mu dauki mataki a kan shawarwarin da kwamitin za su tattauna kuma su ba mu.
Aminiya: Ko za ka yi mana takaitaccen bayani a kan halin da ake ciki a Jihar Borno yanzu domin wasu na cewa kila har yanzu ana nan gidan jiya?
Gwamna Shettima: Mahukaci ne kawai zai ce har yanzu ana gidan jiya amma duk mai hankali ya san muna gani a kasa. Domin a cikin wata ukun nan aka kwato Gamborun Ngala da Kalabalge da Dikwa da Mafa da Banki da Kumshe. Duk a cikin watan uku aka kwato su. Mun gani a kasa gaskiya ba kamar a da ba. Akwai canje-canje domin Babban Hafsan Sojojin Najeriya a kusan mako biyu da suka wuce a mota ya tashi daga Abuja ya biyo ta Jos da Bauchi da Gombe ya shigo ta Biu zuwa Buratai har ya isa Buni-Yadi duk a cikin mota.  Ka ga ke nan ya nuna kuzarinsa, kai Sallah ma an yi tare da shi ne a Damaturu a lokacin watan azumi. Yanzu haka da muke maganar nan yana Maiduguri yau kwanansa biyu a Maiduguri. Ba ya yin wata guda bai shiga Maiduguri ba, ka ga ke nan ai ya nuna kwazo fisabilillahi.
Aminiya: Ke nan dai kana ganin sojojin za su cika wa’adin da Shugaban kasa ya ba su na kawo karshen Boko Haram a watan Disamban shekarar nan?
Gwamna Shettima: Gaskiya ga dukkan alamu kwanakin ’yan Boko Haram sun kusa karewa domin nasarar da sojoji ke samu a kansu nan ba da dadewa ba za a kawo karshen matsalarsu. Koda yake sojojin na dan fuskantar turjiya daga matasan amma dai ga dukkan alamu sojojin na kokari matuka domin korar ’yan ta’addan daga maboyarsu a yankin. Muna kuma yaba wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan goyon bayan da yake bai wa sojojin a wannan ba-ta-kashi da suke yi da ’yan ta’adda.