Yaki da cin hanci ba aikin kwana daya ba ne- Ambasadan Denmark

A ranar Talatar da ta gabata, Ambasadan Denmark a Najeriya Torben Gettermann ya ce yana da muhimmanci ’yan Najeriya su gane cewa yaki da cin hanci da rashawa ba zai faru a dare daya ba. Getterman ya fada wa Kamfanin Dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Legas cewa yakin ganin bayan cin hanci da rashawa […]

Yaki da cin hanci ba aikin kwana daya ba ne- Ambasadan Denmark

A ranar Talatar da ta gabata, Ambasadan Denmark a Najeriya Torben Gettermann ya ce yana da muhimmanci ’yan Najeriya su gane cewa yaki da cin hanci da rashawa ba zai faru a dare daya ba.

Getterman ya fada wa Kamfanin Dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Legas cewa yakin ganin bayan cin hanci da rashawa a kowace kasa abu ne da ake bi da sannu.

A cewarsa, yaki da cin hanci a ko ina yana bukatar fahimta da kwazo na mutanen kasar.

“Ba zance Denmark ita ta fi kowace kasa karancin cin hanci a duniya ba, amma mun yi shekara biyar muna kasa ta daya a wannan lissafin.

“Dole ‘yan Najeriya su sani cewa cin hanci matsala ce da take bargon Najeriya; don haka, sai sun sani cewa yaki da cin hanci ya kamata a yi shi na tsawon lokaci ne,” a cewarsa.

Getterman ya ce kokarin da Shugaba Muhammadu Buhari yake yi wajen yaki da cin hanci da rashawa zai yi tasiri idan ‘yan Najeriya suka sa kansu kyamatar cin hanci da rashawa a aikinsu na yau da kullum.

Ambasadan ya yabi kokarin da Gwamnatin Tarayya take yi wajen haifar da yanayin yin kasuwanci mai sauki.

Ya ce kamfanoni da yawa a kasar Denmark sun nuna sha’awar yin kasuwanci da kuma kara hannun jari a Najeriya.

“Yadda Gwamnatin Tarayya ta Najeriya ta dukufa wajen canja yanayin kasuwanci na kara ma mutane karfin gwiwa.

“Muna kokari wajen ganin cewa kamfanonin Denmark da dama suna kawo abubuwan da ‘yan Najeriya suke bukata,” inji shi.

Ambasaadan ya qara da cewa “muna so mu ga daidaiton kasuwanci tsakanin kasashen nan biyu.”