Yaki da cin hanci: Buhari na bukatar goyon bayan malaman addini – Kadinal Onaiyekan
Bihsop din cocin Katolika na Abuja, Kardinal John Onaiyekan, ya ce bai kamata a dauki yaki da cin hanci da rashawa a matsayin abin ne da gwamnati mai ci ta Shugaba Muhammadu Buhari ta kirkiro ba, maimakon haka a dauke shi a matsayin wani aiki ne da daukacin al’umma ya wajaba ta hada hannu wajen […]
Bihsop din cocin Katolika na Abuja, Kardinal John Onaiyekan, ya ce bai kamata a dauki yaki da cin hanci da rashawa a matsayin abin ne da gwamnati mai ci ta Shugaba Muhammadu Buhari ta kirkiro ba, maimakon haka a dauke shi a matsayin wani aiki ne da daukacin al’umma ya wajaba ta hada hannu wajen samun nasararsa.
Kadinal Onaiyekan ya bayyana haka ne a ranar Asabar da ta gabata lokacin rantsar da limamai da masu wa’azin na cocin Katolika a harabar cocin Catholic Pro-cathedral da ke Abuja.
Kadinal Onaiyekan ya ce akwai bukatar kara zage dantse wajen yaki da cin hanci da rashawa, kuma wannan kokari zai cimma nasara ne kawai idan malaman addini suka goya masa baya.
“Ba Buhari ba ne yake cewa mu yaki cin hanci da rashawa. Muna yin hakan ta hanyoyi da dama. Ina jin za mu iya kara zage dantse wajen yaki da cin hanci da rashawa idan akwai hadin gwiwa a tsakanin gwamnati da cibiyoyin addini. Ba ina magana a kan coci kawai ba ne,” inji shi.
Sai dai Kadinal Onaiyekan ya ce gwamnati mai ci ba ta tsoma shugabannin addini yadda ya kamata a yaki da cin hanci da rashawar.
Ya ce shelar canji na gwamnatin Jam’iyyar APC zai samu nasara ne kawai idan gwamnati ta bayar da dama ta hada gwiwa da kungiyoyin addini wajen yaki da cin hanci da rashawa da ake yi a yanzu.
“Ya kamata a samu wani tsari da jami’an gwamnati da shugabannin addini za su zauna su duba yadda kowa zai tallafa wajen yaki da cin hanci da rashawa. Amma a yanzu ban yi tsammanin akwai wannan hadin gwiwa ba,” inji shi.
Ya kara da cewa: “Idan kana son zukatan jama’a su canja wajibi ne ka hada da mu, mu ne kwararru a wannan fanni.”
Kadinal Onaiyekan ya ce duk da haka wajibi ne shugabannin addini su taimaka wajen yaki da cin hanci da rashawa. “Duk da cewa ba za mu jira su gaya mana ba, abin da na yi imani shi ne idan aka kara kokarin yin aiki tare nasarar da za a samu za ta fi haka,” inji shi.
Sai ya ce rantsar da limamin na nuni ne da aukuwar wani abin alheri a kasar nan. Kuma ya bukaci sababbin limaman su mike tsaye a daidai wannan lokaci da ake komawa ga bautar abin duniya.
Wadanda aka rantsar din sun hada da Rabaran bincent Iletogbe da Rabaran Kefas Magaji. Sai Charles Eketelu da Kingsley Fedinand da Emanuel Odiong da Joseph Tyopenda da John Uche da Naset Nwodo da kuma James George.