Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa A Najeriya: Nazari a mahangar Musulunci (3)

Wannan lacca ce da aka gabatar a ranar 26-9-2016, don kara wa juna sani da Babban Lauya Ustaz Yusuf Alaoye Ali (SAN) ya gabatar a wani taro da ake shiryawa duk shekara mai taken ‘Muslim Legal Year Serbice’ a babban Masallacin Egba, Kobiti, Abekuta, Jihar Ogun. Barista M.B. Mahmoud Gama (08130969818) ne ya fassara. Cin […]

Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa A Najeriya: Nazari a mahangar Musulunci (3)

Jami’an ‘yan sandan Najeriya a bakin aikin bincike a hanya

Wannan lacca ce da aka gabatar a ranar 26-9-2016, don kara wa juna sani da Babban Lauya Ustaz Yusuf Alaoye Ali (SAN) ya gabatar a wani taro da ake shiryawa duk shekara mai taken ‘Muslim Legal Year Serbice’ a babban Masallacin Egba, Kobiti, Abekuta, Jihar Ogun. Barista M.B. Mahmoud Gama (08130969818) ne ya fassara.

Cin Hanci Da Rashawa a Hukumar ’Yan Sanda:

To fa, babbar magana, ka ji shakundum! Idan aka ce cin hanci da rashawa a hukumar ’yan sanda, to ta ina za mu fara? Ta karbar ‘na-goro’ ko ta cin zali, ko ta yin lalata da matan da aka tsare a caji-ofis ko kuwa ta mayar da fari baki wajen aiwatar da binciken masu laifi? Akwai wata shahararriyar magana da ake cewa, dan sanda abokin kowa, to amma haka abin yake a Najeriya? Mu dai a kasar nan, ’yan sanda tamkar abokan gabarmu suke saboda a mafi yawan lokuta za ka same su kiri-kiri suna mayar da fari baki da zarar an sinna musu ‘na-goro.’  Saboda mummunar ta’adar ’yan sandan Najeriya, ta-kai-ta-kawo har nagari daga cikinsu ma ba a la’akari da su a yayin bambance nagari da mugu daga cikinsu, kudin goro kawai ake yi musu!

’Yan sanda masu kafa shingaye a titunanmu, suna amfani da wannan dama wajen amsar ‘na-goro’ daga masu ababen hawa ne kawai amma ba don kawo tsaro da jin dadin masu amfani da hanyoyin ba. Ba da na-goro ga ’yan sanda sai ya zama farilla, koda kuwa direba yana da cikakkun takardun motarsa; in kuwa ba haka ba su bata maka lokacin gudanar da harkokinka, in kuwa dan kiya-kiya ne kai, ka kasa hada na balas a wannan rana. Sun zama a wajen dirobobi tamkar bawa da ubangidansa, sai yadda suka yi da su.

Abubuwan da Suke Janyo Cin Hanci da Rashawa:

Wai shin me ke haddasa cin hanci da rashawa ne? Abubuwa da dama ne kan haddasa da kuma ta’azzara wannan mummunar dabi’a ta cin hanci da rashawa. Kadan daga cikinsu su ne rashin wadatar zuci ko rashin godiyar Allah da rashin samar da kyakkyawan tsari ga ci gaban matasa da talauci da kuma rashin aikin yi.

Rashin wadatar zuci ko rashin godiyar Allah ya haifar da matsaloli da dama a mafi yawan kasashen duniya, ciki har da Najeriya. Wannan ya sa shugabanninmu na soja a lokacin mulkinsu da na siyasa daka wasoso a kan dukiyar ’yan kasa, wanda ya kamata a yi amfani da su wajen gina al’umma amma suka wawashe (ko kuma suna kan wawashewa) don gina kansu kawai; wanda hakan ya haifar da mummunan koma-baya ga kasar da kuma al’ummarta baki daya.

Rashin kyakkyawan tsari a ci gaban matasa da samar da wani takamaiman tsari ga matasa don su tsaya da kafafunsu, ya taka rawar gani wajen yawaitar rashin gaskiya da cin amana, kamar su yin damfara ta hanyar intanet da fyade da sauransu, a tsakanin matasanmu. Duk wadannan suna faruwa ne saboda gwamnatocin Najeriya sun kasa fahimtar muhimmancin taimaka wa matasa don neman na kansu. A duk lokacin da iyaye da gwamnatoci suka karfafi matasansu ta fuskar ba su tarbiyya da karfafarsu ta hanyar koya ko inganta sana’ao’insu, to babu shakka za a dakile kaifin ko ma a kakkabe wannan annoba daga al’ummarmu baki dayanta.

Talauci, suka ce wai aminin kafirci! Ma’ana, duk inda ka ga talauci idan ka bincika da kyau, to za ka ga kafirci ko kuma burbushinsa. Karbabben kiyasi na duniya ya nuna cewa duk mutumin da yake rayuwa kasa da Dalar Amurka 1:25 (Kwatankwacin Naira 360.25), a rana, to za a iya cewa wannan mutumin talauci ya cin masa! To a Najeriya akwai mutane da dama da suke rayuwa a kan haka (N360.25), ko ma kasa da haka, wadanda hakan ya jefa su cikin aikata munanan dabi’u, ciki har da cin hanci da rashawa. Misali, inda za ka ga an tura mutum don ya kashe wani, don yin tsafi ko kuma wani dalili na siyasa, a kan Naira N10,000 ko ma kasa da haka, ko kuma ka ga ana amfani da matasa wajen bangar siyasa a kan kudin da ba su taka kara sun karya ba, duk saboda katutun da talauci ya yi wa matasa.

Rashin aikin yi daya ne daga cikin manyan kalubalen da suka dade da nanike wa ’yan Najeriya tsawon lokaci.  Mutane da dama sun afka cikin halin cin hanci da rashawa saboda rashin aikin yi da ya dade yana addabarsu. Abu ne mai sauki ga mutumin da yake dan zauna-gari-banza da ya tsinci kansa cikin kowane irin rashin gaskiya da rashin imani don ya samu kudaden da zai tallafi rayuwarsa da su, ta yadda daga karshe yin hakan ba zai haifa wa al-umma da-mai-ido ba.

Illolin Cin Hanci da Rashawa Wajen Gina Kasa:

Illolin suna da yawa amma kadan daga cikinsu akwai rashin zuba jari daga ’yan kasashen waje da yawaitar talauci da rashin ci gaban kasa da kuma yawaitar rikice-rikice a kasa.

Rashin aikin yi a Najeriya zai ragu matuka idan da a ce an karfafa gwiwar masu zuba jari daga kasashen waje don su zo su zuba jarinsu. To amma sai ga shi masana’antun da suka kamata su zuba jarinsu a Najeriya suna ki yin hakan saboda tsoron da suke da shi na rushewar dukiyarsu, ba ma maganar su sami riba ba saboda dalilin cin hanci da rashawa da ya yi wa kasar katutu, wanda hakan ya ta’allaka ga rashin tsaro da halin rashin tabbas da kasar ke fuskanta a kodayaushe. Wannan ta sa ba sai mun fada ba, babu wani mai sanya hannun jari mai cikakken hankali da zai aminta ya zuba dukiyarsa a kasar da ta yi auren zobe da rashi tsaro!

Yawaitar Talauci: A duk sa’ar da jami’an hukumomin gwamnati da na masu zaman kansu suka mayar da hankali wajen daka wasoso ga dukiyar jama’a, to babu abin da yin haka zai haifar sai durkushewar wadannan hukumomi, wanda daga karshe zai hannunta talakawa ga rashin aikin yi wanda daga bisani talauci ya shige su, in ma ba a yi hankali ba, ya shige su irin shigar nan ta sojan Badakkare.

Rashin Ci Gaban Kasa: Duk kasar da karanta ya kai tsaiko cikin cin hanci da rashawa kamar Najeriya, to babu shakka akwai yiwuwar za ta fuskanci mummunan koma-baya dangane da ci gabanta. Duk lokacin da aka ce manyan jami’an gwamnati da na masana’antu masu zaman kansu ba abin da suka sani sai azurta kansu ta hanyar handame dukiyar jama’a zuwa kasashen waje to babu shakka tattalin arzikin wannan kasa zai shiga kwaranniyar da ba a san lokacin fita daga cikinsa ba.

Rikice-Rikice a Cikin Kasa: Shin ko kun san cewa duk tashe-tashen hankalin da ke afkuwa nan da can a cikin Najeriya kama daga rikicin ’yan Boko Haram da ’yan garkuwa da mutane; da na ’yan Neja-Delta, da na makiyaya da manoma zuwa ta ’yan Biyafara, duk sun wanzu ne saboda cin hanci da rashawa, wato rashin gaskya da kin yin abu bisa ka’ida? Duk wadannan rikice-rikice sun haifar da mummunan tasiri da dakile ci gaban tattalin arzikin kasar nan ta hanyar fatattakar ’yan kasashen waje masu niyyar zuba hannayen jarinsu don ci gaban tattalin arzikin kasar.