Yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya: Nazari a mahangar Musulunci (5)
Wannan lacca ce da Babban Lauya Ustaz Yusuf Olaoye Ali (SAN) ya gabatar a wani taron kara wa juna sani da ake shiryawa duk shekara mai taken ‘Muslim Legal Year Serbice’ da aka gabatar a ranar 26-9-2016, a babban Masallacin Egba, Kobiti, Abekuta, Jihar Ogun. Barista M.B. Mahmoud Gama (08130969818) ne ya fassara. Yin imani […]
Wannan lacca ce da Babban Lauya Ustaz Yusuf Olaoye Ali (SAN) ya gabatar a wani taron kara wa juna sani da ake shiryawa duk shekara mai taken ‘Muslim Legal Year Serbice’ da aka gabatar a ranar 26-9-2016, a babban Masallacin Egba, Kobiti, Abekuta, Jihar Ogun. Barista M.B. Mahmoud Gama (08130969818) ne ya fassara.
Yin imani da Allah da sakankancewa da cewa Shi ne Mahalicci Mai kaddarawa, Mai arzutawa, Mai talautawa, yana da muhimmanci a rayuwar dan Adam. Rashin imani da kin yarda da Allah cikin wadancan siffofin naSa, kamar yadda muke nunawa a aikace, shi yake jagora zuwa ga fadawa cikin wannan mummunar ta’ada ta cin hanci da rashawa a kasar nan. Matukar ma’aikacin gwamnati ko duk wanda aka danka wa wata amana ta al’umma zai yi imani da Allah da sakankancewa da cewa Allah Shi ne Mai azurtawa, kuma Mai talautawa – sakankancewa ta hakika, to ba ta yadda za a yi ka same shi yana handama da babakere cikin abin da aka danka masa na amana. Allah cikin LittafinSa Mai girma (K:65:2-3) Yana cewa:
“…kuma duk wanda ya ji tsoron Allah, to (Allah) zai sanya masa mafita (a duk al’amuransa). Kuma Ya azurta shi ta inda ba ya zato. Kuma duk wanda ya dogara ga Allah (da sakankancewa a gare Shi) to, Allah Ya isar masa….”
Hakika abin dubawa ne cewa a cikin wannan al’umma tamu, tsoron Allah ya yi karanci, in ma ba a ce babu shi kwata-kwata ba, a zukatanmu. Hakan kuwa ya hada da wadansu malaman addinan nan biyu (Musulunci da Kirista), wadanda a ka’ida su ne ya kamata su dasa mana jin tsoron Allah a zukatanmu ta hanyar wa’azozinsu. Soyayyar abin duniya da kyale-kyalen rayuwa, su suka yi katutu cikin zukatanmu. Mafi yawan mutane, muka zama bayi ga wannan duniya mai karewa, ta yadda muke ganin wadanda suka samu arzikin duniya da rayuwa mai kyau a matsayin wadanda Allah Ya yi wa gamo-da-katar, ba tare da yin tunani ta yaya suka tara wannan dukiya ba. To shi ke nan mu ma sai mu tsunduma tare da kudurcewa a rai, ko ta halin kaka sai mun tara irin wannan dukiya ta hanyar wa-ka-ci-ka-tashi da baitul malin kasa ta hanyar kowane irin nau’in cin hanci da rashawa da ya zo mana a rai.
Tabbatar da adalci da daidaito a tsakanin mutane
A Musulunci akan iya rusa tsarin cin hanci da rashawa ta hanyar tabbatar da adalci, wanda shi ne kashin bayan tabbatar kowace kasa da ke doron duniyar nan. Tabbatar da adalci da daidaito a tsakianin mutane a Musulunci shi ne, da farko a dasa tsoron Allah a cikin zukatan mutane, sannan a samar da daidaito cikin rabon arzikin kasa da kuma sama wa mutane ababen gudanar da rayuwarsu na tilas da kuma kange masu karfi daga zaluntar marasa karfi, a cikin al’umma. Dabbaka wannan tsari yadda ya kamata a cikin al’umma shi ne hanya dodar ta fatattakar cin hanci da rashawa a cikin al’umma.
Har ila yau, tsarin adalci da daidaito a tsakanin mutane irin na Musaulunci, yana sa shugaba ya rika kudurcewa a koyaushe cewa, shi fa mai hidima wa jama’a ne ta hanyar inganta rayuwarsu da umartarsu da aikata kyakkyawan ayyuka kuma akwai ranar da Allah zai titsiye shi don yin bayanin yadda ya gudanar da wadanda yake mulka din. Annabin rahama (SAW) yana cewa:
“Duk shugaban da aka damka wa jibintar al’amuran Musulmi amma bai inganta rayuwarsu ta duniya da ta Lahira ba, sannan ba ya damuwa da jin dadinsu, to ba zai shiga Aljanna ba.”
Sannan adalci da daidaito irin na addinin Musulunci yana koyar da shugabanni gudanar da mulki a bayyane (ba tare da yaudara ko nuku-nuku ba), da kuma yin gaskiya a yayin gudanar da mulkinsu. Annabi Muhammad (SAW) yana cewa:
“Duk wanda daga cikinku muka danka wa shugabanci, a kan wani abu, kuma ya ha’ince mu kwatankwacin allura ko kasa da haka, to ya yi almundahana kuma sai ya biya shi a gobe Kiyama.”
Gaba daya dai ka iya cewa, tabbatar da adalci da daidaito a tsakanin mutane yana tabbatar wa dan Adam cewa shi wakilin Allah ne a ban-kasa, sannan shi zai yi bayani a kan duk abin da ya zaba kuma ya aikata a wannan duniya. A gobe Kiyama, yin imani da tsayawa a gaban Allah don bayar da bahasi a kan duk abin da mutum ya aikata a gaban Allah, yana sa dan Adam bin dokokin Allah da guje wa duk wani sabon Allah da zalunci da duk wani nau’i na cin hanci da rashawa. Ba ta yadda za a yi cin hanci da rashawa su ci gaba da habaka a cikin al’ummar da ta yi imani (imani na hakika) da haduwa da Mahaliccinta a gobe Kiyama. Annabi (SAW) yana cewa:
“Ina yi muku kashedi da cin hanci (da rashawa), domin cin hanci kafIrci ne, sannan shi mai bayar da ita, ba zai ji kanshin Aljanna ba.”
Kammalawa:
Shawarwari domin samun mafita
Mun riga mun san cewa cin hanci da rashawa, babbar dadaddiyar matsala ce da ta dade tana addabar al’ummai ciki har da al’ummar Najeriya. Mun riga mun san cewa, cin hanci da rashawa ya hada da duk wata mu’amala wacce babu tsoron Allah a cikinta, ko rashin halin kirki, ko kin aikata abu yadda ya kamata, ko kin tabbatar da adalci da daidaito a tsakanin mutane a yayin mulkarsu, ko kawo tarnaki cikin ci gaban al’umma da walwalarsu. A daya hannun kuma, mun san cewa Musulunci ya samar da cikakkiya da fayyatacciyar mafita, ba ma ga cin hanci da rashawa ba kawai, a’a har ga duk wata matsala da damuwa da suka addabi dan Adam a bayan kasa. Kari a kan haka, zan so in bijiro da wasu hanyoyi don lizimta wa kanmu da gwamnati da kuma duk wani mai-ruwa-da-tsaki a cikin yakar wannan ta’ada ta cin hanci da rashawa.