Yaki da cin hanci da rashawa: A yi bincike sosai

A wannan mako ma muna dauke da gudunmawar wani makarancin mu ne Malam Usman Musa Gabari mai lambar waya 08033510179, dagaKano da yake ganin ya kamata shirin yaki da cin hanci da rashawa ya hado da manyan zarge-zargen almundahanar da ake zargin an yi tun daga zamanin mulkin Janar Babangida har zuwa lokacin Jonathan domin […]

Yaki da cin hanci da rashawa: A yi bincike sosai
Yaki da cin hanci da rashawa: A yi bincike sosai

A wannan mako ma muna dauke da gudunmawar wani makarancin mu ne Malam Usman Musa Gabari mai lambar waya 08033510179, dagaKano da yake ganin ya kamata shirin yaki da cin hanci da rashawa ya hado da manyan zarge-zargen almundahanar da ake zargin an yi tun daga zamanin mulkin Janar Babangida har zuwa lokacin Jonathan domin a hukunta wadanda aka samu da laifi tare da wanke marasa laifi kowa ya huta. Ga abin da yake cewa:

Lokacin da ake gab da cika kwanaki 100 da kama madafun ikon masu rike da ragamar mulkin Najeriya na yanzu, daya daga cikin manyan alkawuran da gwamnatin Jam’iyyar APC a karkashin jagorancin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta dauka shi ne yaki da cin hanci da rashawa ko almundahar kudin gwamnati.
A cikin wadannan kwanaki da ba su cika kwana 100 ba, duk wanda yake kasar nan da ma kasashen waje, idan zai yi adalci ya san matakan da gwamnatin take dauka sun nuna da gaske take.
Illar cin hanci da rashawa a bayyane take, domin ita ce take dakile ci gaban kowace kasa, ta jefa al’umma cikin kuncin rayuwa da mummunan talauci da karyewar tsarin ilimi da kiwon lafiya, kuma ita take sabbaba rashin tsaro kamar yadda muke ciki a Najeriya.
Saboda kudin da ya kamata a sayi kayan aiki ga jami’an tsaro, a kula da walwala da jin da dadinsu, don su samu kwanciyar hankalin da za su yi aikinsu da karfin jiki, sai wasu ’yan tsirari sun kwashe su kimshe su! Kudin da za a sayo kayan aiki a inganta asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya, a kula da likitoci da jami’an lafiya, sai wasu su kwashe! An bar likitoci da jami’an kiwon lafiya kullum suna yajin aiki, wasu ma suna ficewa zuwa kasashen waje, saboda an kasa rike su a kasarsu ta haihuwa. Marasa lafiya suna mutuwa, saboda rashin ingantaccen tsarin kula da lafiya. Kusan karama da babbar cuta duk daya ne a wurin talakan Najeriya, don ba ya da kudin sayen magani, ko bincike da gwaje-gwajen lafiya, a asibitoci masu zaman kansu, yayin da a asibitocin gwamnati kuma babu wannan dama saboda rashawa! Haka abin yake a bangaren ilimi, babu kayan aiki da kulawa, saboda dan abin da ake warewa a kasafi yana zurarewa ne zuwa aljifan wasu kafin dan kyas ya kai inda aka tura shi.
Wannan misali ne na illar da almundaha da satar kudin gwamnati ke haifarwa wajen kashe kasa da al’ummarta. Satar nan kowa ya san hanyoyinta suna da yawa, a fitar da kudi don yin wani aiki a bangaren lafiya ko ilimi ko tsaro, ya zamo ba a yi aikin ba, kuma a rasa inda kudin suka shiga. Wannan ya sha faruwa a tarayya da jihohi da kananan hukumomin kasar nan. Ko kuma a fitar da kudin amma aikin da za a yi ba zai fi na kashi 20 cikin 100 ba, kashi 80 na kudin duk yana karewa ne a wani sakon aljifan mutane. Ko kuma a ba da kwangiloli ga wasu shafaffu da mai, aikin da bai wuce a yi mai inganci a kan Naiar 100 ba, sai a ba da shi a kan Naira 1000, kuma a yi shi bai kai ingancin na  Naira 100 ba. Ko kuma su shugabannin su ba da kwangila da sunan wani ko wani kamfani, amma ta karkashin kasa kansu suke bai wa, su za su yi. Wanda aka yi amfani da sunansa ko kamfani bai wuce dan kamasho ba. Wannan shi ne abin da yake faruwa a kusan kowane sashi na gwamnati. Kamar yadda kwamitin Ahmad Joda ya tabbatar cewa: “Rashawa ta shiga kusan kowane sashi na gwamnati ta lalata shi!” Shugaba Muhammadu Buhari ma ya yi makamanciyar wannan magana.
Alhamdulillah, yaki da rashawa yana cikin muhimman dalilan zabar Shugaba Muhammadu Buhari, kuma ya nuna da gaske yake yi, ya kamata ’yan Najeriya su goyi bayansa ta duk hanyar da za su iya har Allah Ya sa a kai gaci.
Abu daya da ni nake ganin ya kamata wannan gwamnati ta sake dubawa shi ne, batun cewa gwamnatin da ta wuce ta Goodluck Jonathan kadai za ta bincika game da zargin almundahana da satar kudin gwamnati, ina ganin zai fi kyau a binciki duk gwamnatocin da ake zargi. Akwai zarge-zarge sanannu a wurin ’yan Najeriya da ake yi wa wasu gwamnatoci da suka wuce. Misali Dala biliyan 12 da aka ce an samu rara a lokacin Yakin Tekun Pasha a gwamnatin Janar Babangida da ake ganin an yi almundahanarsu; sai zarge-zargen da ake yi wa gwamnatin marigayi Janar Abacha da zargin da ake yi wa gwamnatin Janar Abdussalami Abubakar game da yadda aka yi da kusan Dala biliyan 43 da aka ce gwamnatin Abacha ta tara; ga kuma zargin da ake yi na kashe Dala biliyan 13 na gyaran lantarki a lokacin Obasanjo, amma babu aikin ba kudin! Ga Dala biliyan 20 da tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya ya yi zargin bacewarsu a gwamnatin Jonathan. Duk wadannan da ire-irensu sanannun zarge-zarge ne ga duk ’yan Najeriya.
A ra’ayina ya kamata a binciki ire-irensu don tabbatar da cewa shin zargin gaskiya ne ? Idan gaskiya ne sai a hukunta mai laifi gwargwadon laifinsa, idan kuma ba gaskiya ba ne sai a bayyana, ka ga su ma wadanda ake yi wa zargin an wanke su daga zargin da ake kallon su da shi.
Fatanmu dai shi ne Allah Ya taimaki Shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa kyawawan manufofinsa na dora Najeriya a kan gwadaben da ’yan kasar za su bugi kirji su yi alfahari da kasarsu a duk inda suke a duniya.