‘Yaki da cin hanci ya hana a biya ma’aikata albashi a watan da ya wuce’

Jam’iyar PDP dake mulki a Najeriya ta ce “Shugaba Goodluck Jonathan ya taka rawar gani ta fannin yaki da cin hanci da rashawa, ba kamar yadda masu hamayya suke bata sunansa da cewa ya gaza ba. Shi ne ya bullo da sabon salon dakile miyagun hanyoyin rabon takin zamani ga manoma da cuwa-cuwar sayar da […]

‘Yaki da cin hanci ya hana a biya ma’aikata albashi a watan da ya wuce’
‘Yaki da cin hanci ya hana a biya ma’aikata albashi a watan da ya wuce’

Jam’iyar PDP dake mulki a Najeriya ta ce “Shugaba Goodluck Jonathan ya taka rawar gani ta fannin yaki da cin hanci da rashawa, ba kamar yadda masu hamayya suke bata sunansa da cewa ya gaza ba. Shi ne ya bullo da sabon salon dakile miyagun hanyoyin rabon takin zamani ga manoma da cuwa-cuwar sayar da kamfanonin gwamnati da hukumar wutar lantarki da tsara rabon kwangilolin gwamnatin tarayya da aka yi miusu kwaskwarima da kwangilolin sayo makamai, wadanda yanzu aka mayar da su tsakanin gwamnatocin kasa da kasa da babu wani dan kamasho a tsakani da kuma batun kasa biyan ma’aikata albashi a watan jiya, wanda ba rashin kudi ne ya haifar da hakan ba sai dai an yi ne domin a kawar da matsalar cin hanci da rashawa a cikin al’amarin.”

Bayanin haka ya fito ne daga bakin Mataimakin Daraktan yada labarai na kwamitin yakin neman sake zaben shugaban kasa Alhaji Isa Tafida Mafindi, cikin hira da wakilinmu jim kadan bayan kammala kamfe a birnin Ibadan a ranar litinin da ta wuce. Ya ce, “ba rashin kudi ne ya haifar da kasa biyan ma’aikata albashi a wasu ma’aikatu a cikin watan jiya ba, sai dai an yi hakan ne domin dakile miyagun hanyoyin sace kudaden jama’a wanda Shugaba Jonathan ya fito fili ya bayar da hakuri game da aukuwar hakan kuma ya nemi hadin kan jama’a domin cimma wannan buri na sa da zai amfani al’ummar kasar a nan gaba.”
A wajen wannan gangami ne Shugaban Jam’iyar PDP na kasa, Alhaji Adamu Mu’azu ya mika wa Sanata Teslim Folarin tutar tabbatar masa da matsayin dan takarar Gwamna a Jihar Oyo a zabe mai zuwa. Jiga-jigan PDP da suka yi jawabai a wajen taron sun hada da Minista a ma’aikara Abuja FCT Uwargida Olajumoke Akinjide da Gwamnan Jihar Ondo Olusegun Mimiko da makamatansu. Daga bisani Shugaba Goodluck Jonathan tare da tawagarsa suka dunguma zuwa birnin Abeokuta domin gudanar da irin wannan taro a Jihar Ogun.